Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Kashe Sama Da Miliyan 356 Kan Noma – Alh. Kabiru

Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Kashe Sama Da Miliyan 356 Kan Noma - Alh. Kabiru

0 92

Gwamnatin jihar Jigawa ta kashe kudi fiye da naira miliyan 356 wajen gudanar da shirin noman dan riba na cluster a 2016.

Kwamishinan aikin gona da albarkar kasa na jiha Alhaji kabiru Ali ya sanar da hakan ta cikin shirin radio Jigawa na musamman na cikar gwamnati shekaru biyu da rabi akan mulki.

Karanta wannan: Wani Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Zai Tsaya Takarar Shugaban Kasa a 2019

Yace wasu manoman na cluster sun bada kudi wasu kuma sun bada kayayyakin amfanin gonar da suka nomaka biya basukan kudaden yayinda wasu kuma suke biya sannu a hannu.

Alhaji Kabiru Ali ya kara da cewar gwamnati ta kuma kashe kudi naira miliyan 516 wajen noman alkama na cluster a 2016 inda nan ma manoma suka fara biyan kudaden basukan da aka basu.

Yace an kuma kashe kudi fiye da naira miliyan 577 wajen gudanar da noman shinkafa yar rani a 2017 inda tuni wasu manoman suka biya basukan da suka karba.

 

Karanta wannan: Za Mu Baiwa Buhari Kuri’u Miliyan 5 Idan Ya Tsaya Takara a 2019 – Ganduje

Yace an kuma kashe kudi kusan naira miliyan 736 wajen shirin noman cluster a 2017 wanda tuni wasu manoman sun fara biyan kudaden da suka karba na shirin.

Yace gwamna Badaru Abubakar ya bada umarnin kara yawan hecta ta noman cluster daga hamsin a kowace mazabar kamsila zuwa hecta hamsin domin kara shigo da alumma cikin shirin.

Alhaji Kabiru Ali ya ce gwamnatin jiha ta samar da takin zamani tan dubu ashirin da daya da dari hudu da hamsin daga cikin tan dubu hamsin da gwamna Badaru Abubakar ya yi alkawarin samarwa manoman jihar Jigawa.

 

Karanta wannan: Miji Ya Kashe Matarshi Kuma Uwar ‘Ya’yanshi Guda 5 da Adda

Yace takin ana sayar dashi akan kudi naira dubu biyar da dari biyar akan kowane bahu.

Yace gwamnatin jiha ta kawo injuna da naurorin sarrafa kayayyakin amfanin gona daban daban da motocin tantan da maganin kwari da ingantattun iri daga kasashen waje domin bunkasa alamurran aikin gona a jihar.

Akan batun ciyawar kachalla kuwa maaikatarsa da maaikatar kare mahalli sun gudanar da aikin cire ciyawar kachalla domin baiwa manoman damar noma abinci.

 

Karanta wannan: Sirikina Ne Ya Cancanta Ya Gaje Ni – Gwamna Okorocha

Yace an yiwa dabbobi kusan miliyan daya da dubu dari hudu da sittin da bakwai rigakafin cutukan dabbobi a 2017 yayinda a wannan shekara gwamna Badaru Abubakar ya bada kudi naira miliyan tara domin gudanar da hujin dabbobi inda ake sa ran yiwa dabbobi miliyan biyu rigakafi a sassan jihar.

Akan batun kiwon awaki kuwa kwamishinan yace an raba awaki uku uku ga zawarawa dubu biyar da dari bakwai da arbain wanda a yanzu haka an fara karbar bashin wadanda aka baiwa a kananan hukumomi takwas wanda ake sake baiwa wasu matan zawarwa.

 

Karanta wannan: Dubban Jama’a Sun Sauya Sheka Daga Jam’iyyar PDP Zuwa APC A Kwara

Yace saboda wannan tsari gwamnatin tarayya ta kwaikwayi jihar Jigawa domin aiwatar da shirin wanda hakan ya sanya gwamna Badaru Abubakar ya bada umarnin kara yawan zawarawan da zasu cigajiyar shirin.

Jihar Jigawa tana da fadin hecta miliyan daya da dubu dari takwas ta noma daga cikin kadada miliyan biyu da rabi da jihar take dashi.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...