Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Hanyoyin Kula Da Lafiyar Jikinka A Lokacin Hunturu

0 443

Yanayin hunturu, yanayi ne dake zuwa da sanyin iska wanda ake yawan samun kura musamman a arewacin Nijeriya.

Yanayin hunturu yana zuwa da wasu tsarabe tsarabe kamar su fashewar jiki, murra, fason kafa, wanda ke barazana ga lafiyar jikin dan Adam

Ga wasu hanyoyi guda 10 da zasu taimaka maka wajen gina lafiyar jikinka a lokacin sanyi

1) Sanya tufafin masu nauyi wanda zasu taimaka wajen magance sanyin
2) A rage sanyawa daji wuta ko kona itace
3) A yawaita cin kayan marmari irinsu lemu, Ayaba, ganyayyaki
4) A dinga wanke kayan ganyen da kyau domin fidda dati da kwari
5) A dinga cire duk wani soket dake hade da wutar lantarki
6) Kada ayi amfani da sabulun fidda kuraje Medicated/Antiseptic
7) A dinga shafawa jiki mai kamar su Vaseline
8) A dinga shafa vaseline ko lip gloss a lebe don hana fashewa
9) Shafa man gashi nada matukar amfani ga mata don hana gashi kakkabewa
10) A dinga sanya hula a kai, kallabi da kuma safar kafa dana hannu.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...