Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Haramta Amfani Da Motoci Masu Aiki Da Man Fetur A Faransa: Babbar Barazana Ga Kasashe Masu Albarkatun Man Fetur

791

Ministan ma’aikatar kare muhalli na kasar Faransa, Nicolas Hulot ya bayyana cewa gwamnati za ta haramta amfani da motoci da sauran injina da ke aiki da man fetur a kokarinta na nuna jajircewarta wajen tabbatar da gyara kan gurbatar yanayi da aka yi wa lakabi da Paris Agreement

 

Zuwa yanzu dai, motaci masu aiki da wutar lantarki da kuma man fetur na da kaso 3.5 cikin 100 a kasuwannin motoci a kasar ta Faransa, inda motocin da ke aiki da lantarki zalla ke da kaso 1.2

 

Takaita bukatar kasar Faransa a sayen fetur da man dizil, zai sanya al’umma ta rage sayen motoci masu aiki da man, wannan kuma ko shakka babu zai shafi farashin man fetur na duniya

 

Sabon shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya nada Hulot a matsayin ministan kare gurbatar yanayi ne saboda Hulot din fitaccen dan gwagwarmaya ne wajen yaki da gurbatar yanayi. Shugaba Macro dai ya kalubalanci shugaba Donald Trump na Amurka kan manufofinsa na yaki da gurbatar yanayi, inda ya kalubalance Trump da ya yi yunkuri wajen “Mayar Da Duniyarmu Madaukakiya”

 

“Yaki da gurbatar yanayi ba shi da wata alaka da wane ne ya ci zabe a wata kasa ko kuma waye ke mulkin wata kasa. Kamata ya yi a ce duk kasar da ta sanya hannu akan yarjejeniyar kawo karshen gurbatar yanayi, ta bayar da gudumawar da ta alkawarta za ta bayar a kunshin yarjejeniyar”

 

“Bana jin Shugaba Donald Trump ya duba  kunshin yarjejeniyar kafin ya yanke hukuncin da ya yanke. Dole da ma za a samu sabuwar gwamnati, amma kunshin yarjejeniyar da ya shafi kasa da kasa baya sauyawa.”

 

Ficewar Donold Trump daga yarjejeniyar Paris kan batun gurbatar yanayi shi ne ya kawo shirin Faransa na daina amfani da mota mai aiki da man fetur

 

Hulot ya ci gaba da cewa “Faransa za ta zamto kasar da ba ta dauke da hayakin man fetur a shekarar 2050. Domin tabbatar da haka, dole sai gwamnati ta zuba jari a harkar”

 

“Tuni dai kamfanin Volvo ta fitar da sanarwar fara kera motoci masu aiki da lantarki a shekarar 2019” Hulot ya tabbatar

 

“Ina da yakinin cewa, kamfanonin kera motoci mallakar kasar Faransa za su bi sahun Volvo. Kamfanoni kamarsu Peugeot-Citreon da Renault, duk da dai abu ne ba dan karami ba, amma za mu je wurin da muke nufin zuwa”

 

Kasar Norway, wacce ita ta fi kowace kasa yawan amfani da motoci masu aiki da karfin lantarki ta bayyana cewa za ta koma amfani da motocin lantarki 100 bisa 100 a shekarar 2025 haka ita ma kasar Netherlands

 

Kasashe Jamus da Indiya suma sun sanya shekarar 2030 a matsayin shekarar da za su koma amfani da motocin lantarki 100 bisa 100

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...