Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Hazaƙar Messi Ta Tsallakar Da Ajentina Zuwa Gasar Cin kofin Duniya A Rasha

0 779

 

Lionel Messi ya jefa kwallaye 3 a ragar masu masaukinsu, Ecuador  a wani yanayi da kafin wasan ya sanya kasar Ajentina cikin halin wataƙillaha su shiga gasar cin kofin duniya da za a buga a ƙasar Rasha a shekarar 2018 ko kuma su gaza shiga gasar sakamakon rashin fara wasannin share fagen shiga gasar da suka yi

 

Tuni dai kishiyar Ajentina, wato ƙasar Barazil ta samu gurbi a gasar ta baɗi, haka nan Uraguay ta samu gurbi bayan da ta doke Bolibiya da ci 4 da 2, inda Luis Suarez ya zura ƙwallaye 2. Sai kuma ƙasar Kwalabiya da ke kan hanyar samun gurbi a Rasha 2018 bayan da ta tashi canjaras da Peru 1 da 1

 

Peru ta ƙare a ta biyar. Wannan na nufin zata buga gida da waje Zealand, sakamakon da zai kai Peru ko Zealand Rasha 2018

Karanta Wannan: Wace ce Wawiyar Mace?

Alexis Sanchez na Arsenal da Chile ba zai buga gasar ta badi ba bayan da hile ta kasa kai bantenta a wasannin share fagen, bayan da Brazil ta lallasa ta da ci 3 da nema a jiya

 

BBC ta rawaito cewa Ajentina ta fara wasan na jiya a matsayin ta 6 a rukuninta wanda haka ke nuna ƙarara ba ta gurbi a gasar na baɗi, kuma sakan 38 da fara wasan Ecuador ta jefa ƙwallon ta hannun Romario Ibarra. Lamarin da ya sake jefa Ajentina cikin hatsarin kasa samun gurbi a Rasha

 

Sai dai minti 12 cikin wasan sai Messi ya farke ƙwallon bayan da Angel di Maria ya bashi wani fasin dage gefen dama

 

Bayan minti 8 da ƙwallon Messi ta farko, sai aljanin naku ya sake zura wata

 

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci kuma sai Messi ya zura ƙwallonsa na 3 cikin bajinta na sai wane da wane, lamarin da ya sa Ajentina ta shallake siraɗi

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...