Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Ayyuriri…: Hukumar Tace Finafinai Da Dab’i Ta Yafewa Jaruma Rahama Sadau

0 593

Shugaban hukumar tace finafinai da dab’i ta jihar Kano, Alhaji Isma’il NaAbba Afakallah ya bayyanawa sashen Hausa na BBC cewa hukumar ta yanke hukuncin yafewa jaruma Rahama Sadau tare da dawo da ita harkar fim bayan da jarumar ta fito ta bayyana nadamarta da kuma neman afuwa ga Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje tare kuma da aika takarda ga kungiyar shirya finafinai ta kasa reshen jihar Kano wato MOPPAN don neman afuwa bisa laifukanta

 

Afakallah ya ci gaba da cewa “Wannan baiwar Allah ta zo ofishina a shekarar da ta wuce inda ta nemi gafara kan abubuwan da ta yi a baya; na gaya mata ta je ta nemi gafarar Gwamna da Sarkin Kano kuma ta fito a gidan rediyo ta nemi afuwarsu da ta al’umar da take ciki.

 

“Don haka a matsayinmu na ‘yan-Adam wadanda kullum muke cikin kuskure, so muke a ja mutum a jiki kada ya fandare, shi ya sa muka yafe mata. Duk lokacin da mutum ya yi laifi ba a rufe masa hanyar tuba. Kuma ko yanzu ta kawo fim za mu tace shi”, in ji shi.

Bude Ka Karanta: Dalilin Da Ya Sa Har Yanzu Bamu Yafewa Rahama Sadau Ba – MOPPAN

 

A watan Oktoban da ya gabata ne shahararriyar jarumar ta fito fili ta nemi gafarar duk wani mutum da bai ji dadi ba sakamakon fitowar da ta yi a wani bidiyon waka tana “rungumar” wani mawaki.

 

A wata wasikar da ta aike wa kungiyar masu shirya fina-finai ta kasa, MOPPAN, Rahama ta nemi afuwa a kan abin da ta yi, tana mai cewa “kuskure ne,” kuma za ta “kiyaye gaba”.

 

A wancan lokacin, Shugaban MOPPAN Kabiru Maikaba ya shaida wa BBC cewa kungiyar za ta sanar da matsayin da ta dauka a kan afuwar da jarumar ta nema bayan shugabanninta sun tattauna a hukumance.

Sai dai har yanzu kungiyar ba ta sanar da matakin da dauka ba.

 

Wata majiya ta shaida wa BBC cewa kan ‘yan kungiyar ya rabu game da batun – inda wasu ke son a yafe mata yayin da wasu suka ki amincewa da hakan.

 

Da alama wannan ne ya sa fitaccen darakta Yaseen Auwal wanda ke goyon bayan jarumar ya nuna matukar bacin ransa game da kafar-ungulun da yake ganin wasu na yi ga batun.

 

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram, daraktan ya yaba wa shugaban hukumar tace fina-finan jihar Kano saboda kokarin da yake yi wurin ganin an dawo da ita fagen fim, sannan ya soki mutanen da ke kawo tsaiko cikin lamarin.

 

A cewarsa, “Allah Sarki bawan Allah Ismai’ila Na’abba, muna kara godiya bisa abin da ka yi a kan Rahama Sadau. Allah ya saka da alheri…ka yi naka mun gode; ka bar mu da ragowar…”.

 

Rahama Sadau, wacce yanzu haka take kasar Cyprus inda take karatu, na shirin fitar da sabon fim dinta mai suna Dan Iya a wannan shekarar.

 Madogara: BBC Hausa
Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...