Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

IGP Idris Ya Roki Kotu Ta Haramta Wa Majalisa Yin Bincike Akan Shi

0 347

Insfekta janar na rundunar ‘yan sandan Nijeriya, IGP Idris ya shigar da kara babbar kotun tarayya da ke Abuja inda ya bukace da ta haramtawa majalisar dattawa yin bincike akan shi.

Sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya sanata Isah Misau dai shi ya zargi IG Idris a zauren majalisar da karbar sama da biliyan 10 a kowane wata daga hannun kamfanoni da wasu attajiran Nijeirya da ake baiwa jami’an tsaro nasu na musamman.

Haka kuma ya zarge shi da karbar tsakanin miliyan 10 zuwa 15 daga hannun kwamishinoni da manyan jami’an hukumar domin a tura su aiki duk inda suke so.

KARANTA WANNAN: An Kama ‘Yan sanda Biyu Da Laifin Fashi Da Makami Da Satar Mutane

Sanata Misau wanda rundunar ta zarga da barin aiki ba bisa ka’ida ba dai a yanzu haka shine shugaban kwamitin majalisa da ke kula da sojin ruwa.

A karar, wacce IG Idris ya shigar ta hannun lauyoyin shi, ya zargi majalisar da fadawa cikin bincike ba tare da tantance ko zarge zargen da ake masa suna da madafa, ba kuma tare da bin ka’idar dokar kasa ba.

Ya na kuma bukatar kotun ta hana majalisar gayyatar shi, zaunar da shi ko yi masa wasu tambayoyi ta kowacce siga, da tattauna zarge zargen tsakanin su da kuma shirya wani rahoto akan batun har sai an saurari karar.

Shugaban majalisar, sanata Bukola Saraki dai ya umarci kwamitin majalisar akan da’a da korafe korafen jama’a da tayi bincike akan batun.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...