Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Indonesiya Za Ta Gina ‘Matatar Mai’ Me Karfin Tace Ganga Dubu 10 A Rana

575

Hakan wani yunkuri ne na wannan gwamnatin bisa jagorancin Shugaba Muhammadu buhari na bunkasa tatar danyen man da aka hako a Nijeriya

A cewar shugaban sashen hulda da abokan kasuwancin na hukumar man fetur ta kasa NNPC, Adi Hartadi ya bayyana cewa tuni da shugaban hukamar NNPC, Maikanti Baru  ya sanya hannu akan wata yarjejeniya tsakanin NNPC da PT Intim Perkasa Nigeria Ltd kan hada hannu wajen samar da wannan matata

Baru ya yi bayani game da matatar jim kadan bayan sanya hannu akan yarjejeniyar a Abuja inda ya ce za a gina wannan matata da ke da karfin tace man fetur ganga dubu 10 a kowace rana ne a garin Akwa Ibom da ke kudancin kasar

Maikanti ya ci gaba da cewa gwamnatin Nijeriya a karkashin Shugaba Buhari za ta ci gaba da kashe kudade wajen dawo da kimar matatun mai a Nijeriya

“Gwamnati za ta ci gaba da yin kira ga kamfanoni da su zo sanya hannun jari a harkar tono da tattar man Nijeriya ta yadda kasar da ‘yan kasar za su amfana da dimbin alherin da arzikin man ya kamata ya baiwa kasar 100 bisa 100”

“Matatun da kasar ke da su a halin yanzu da ke da karfin tace akalla ganga 445, 000 a kowace rana ba sa iya aiwatar da wannan aiki na tace abinda matatun ke da karfin tacewa saboda rashin hannun jari da ‘yan kasuwa suka ki saka wa a harkar atsawon shekarun nan”

“A saboda haka ne ma NNPC za ta baiwa wannan kamfani na Indonesiya hadin kan da ya dace don ganin cewa aikin matatar ya tabbata cikin lokacin da aka deba masa”, inji shugaban hukumar NNPC, Maikanti Baru

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...