Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Jami’an Tsaro Sun Samu Muggan Makamai a Gidan Nnamdi Kanu

0 355

Kwamishinan ‘yan sandan jahar Abia Mr Anthony Ogbizi ya ce sun samu muggan makamai a gida shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu a sumamen da suka kai ranar Lahadin da ta gabata.

Kwamishinan ya bayyana haka ne ga manema labarai a jiya Alhamis a babban birnin jahar, Umuahi, inda ya ce makaman sun hada da wata babbar bindiga da boma boman da aka hada da man fetur.

Ya ce sun samu boma boma ne a hade a cikin bokitai, da kuma wasu takardu da wasiku da ke tona asirin ayyukan kungiyar da shirye shiryen su.

Ya ce dama dai sun kai sumamen ne bayan da suka samu bayanan sirri da ke nuna cewa wasu daga cikin mambobin kungiyar sun ci gaba da gudanar da harkokin su duk da haramcin da aka sanya.

KARANTA WANNAN: Rundunar sojin Nijeriya ta yi magana akan inda Kanu ya ke

Ya ce haka kuma sun samu tambarorin Biafra da dama da sandar mukami kuma su na ci gaba da bincike akan su.

A cewar kwamshinan, sun cafke wasu ‘yan kungiyar a sakamakon abubuwan da suka gano a yayin sumamen.

Banda abubuwan da ya bayyana a baya, kwamshinan ya kuma ce sun samu nambobin wayoyin shugabannin kungiyar na yanki yanki kuma za su yi amfani da su wajen yin bincike mai zurfi akan maganganun ‘yan kungiyar da wadanda ke goya masu baya.

 

Tukuicin Juma’a!

Katin MTN: 7383 4066 1766 1769 8301

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...