Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

A Jihar Bauchi, An Yankewa Wasu Maza 2 Hukuncin Daurin Rai Da Rai Bayan Samunsu Da Laifin Aikata Fyade

0 553

Bayan shekaru uku da aikata laifin fyade akan wata mace ‘yar shekaru 40 da haihuwa da aka bayyana sunanta da Zainab Muhammad, tare da kwakule mata ido daya da kuma lalata ragowar dayan da basu cire ba, kotu a jihar Bauchi ta yankewa wasu maza hukuncin daurin rai da rai bayan dukkan hujjoji da shaidu sun tabbatar da cewa su suka aikata laifin da a ke tuhumarsu da shi

 

 

A ranar 1 ga watan Maris, 2014 ne wani Muhammad Sani da aka fi sani da Bambi mai shekaru 30 da haihuwa tare da abokin laifinsa, Sabo Rabo da a ke yi wa lakabi da Bullet ami shekaru 40, suka hada kai wajen aikata laifin, inda suka yi kwanton bauna ga matar akan hanyarta ta komawa gida bayan ta halarci wani biki

 

 

Sun yi amfani da damar rashin jama’a da ke a kan hanyar suka dauke matar suka shiga da ita duhuwa, inda a nan ne fa suka yi ta karba-karba wajen biyan bukatarsu da ita

 

 

Bayan gama aikata fyade ga matar ne sai suka sanya wuka suka cire idon matar na dama tare da lalata na idon nata na hagu, inda daga nan ne suka tafi suka barta ba a cikin hayyacinta ba

 

 

Lamarin dai ya faru ne a wani daji da ke kauyen Lukshi da ke karamar hukumar Dass a lokacin da Zainab ke kan hanyarta ta komawa gida (Yelwan Dawani, karamar hukumar Toro) bayan ta halarci wani biki na nadin sarauta

 

 

Mai shari’a Rabi Umar wacce ita ce alkalin alkalan jihar ta Bauchi ce tabbatar da wannan hukunci akan masu laifin, inda ta bayyana cewa ta samu bukatar neman a yi wa masu laifin sassauci bayan da kotu ta same da aikata laifin, sai dai ta ce ko kusa ko alama masu laifin ba su cancanci sassauci ko tausayawar hukuma ba bayn samunsu da aka yi da laifin aikata fyade, hada kai wajen aikata mugun aiki, jefa rayuwar wani cikin ukuba ta har abada da kuma kokarin aikata kisan kai

 

 

In bamu manta ba a gurfanar da masu laifin ne a ranar 4 ga watan Maris na shekarar 2015. Shekara guda bayan sun aikata laifin

 

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...