Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Kafofin Yaɗa Zumanta: Yadda Saurayin Da Muka Haɗu A Instagram Ya Shayar Da Ni Kwayar Sanya Bacci, Ya Yi Min Fyaɗe, Ya Ɗauki Hotunana Tsirara – Dalibar Jami’a

0 1,580

 

Wata dalibar jami’ar gwamnatin tarayya da ke jihar Ilorin da aka boye sunanta ta bayyanawa manema labarai yadda wani saurayi da suka hadu a shafin Instagram ya ribaceta har ta ziyarce shi zuwa jihar Legas, inda ya kaita wani Otel, inda a nan ne ya sanya mata kwayar sanya bacci a abin shanta, abinda ya bashi damar yi mata fyade babu kakkautawa, bayan ya gama kuma ya dauki hotunanta tsirara

.

Dalibar ta bayar da labarin yadda lamarin ya faru ga manema labarai cikin hawaye, inda ta bayyana cewa: Na hadu da wannan mutum a kafar Instagram, inda ya bukaci da mu zama abokai kafin daga baya ya nemi da na zama budurwarsa

 

Na amshi goron gayyatarsa bayan ya dauki tsawon lokaci yana matsa min, ni kuma ina jan aji kamar dai yadda ya ke a al’adar mace na kin karbar tayin soyayyar namiji farat da garaje

 

 

Na fara haduwa da shi a Legas a lokacin da na je hutu. Bayan wannan haduwa ce sai ya gayyaceni zuwa wani Otel a yankin Ojo da ke jihar Legas din.

 

Bayan na je, mun fara hira, sai ya bukaci da ya yi lalata da ni, inda ni kuma na ce masa ba zan yi ba. Ko kadan bai nuna damuwarsa ba bayan na hana shi abinda ya nema, muka ci gaba da hira. Wannan ya sanya na saki jikina

 

Bayan dan lokaci kadan ya fita ya samo mana abin sha. Muka ci gaba da sha muna hira. A cikin hirar ce ya yi min alkawarin Naira 15,000, kuma nan take ya yi min taransifa ta wayarsa

 

Daga nan fa ban san inda na ke ba, sai tashi na yi na ganni babu kaya a jikina, kuma ina jin wani radadi a gabana alamar ya tara da ni. Kafin hankali ya dawo sai ga wani mai aikin Otel din ya bude ya miko masa kwaroron roba

 

Da na fahimci sake komawa kaina zai yi, sai na yi kururuwar neman taimako, inda a nan ne aka kawo min dauki na samu na fita na bar Otel din jikina duk babu karfi

 

A yammacin ranar da abin ya faru, sai saurayin nawa ya aiko min sako ta kafar WhatsApp, inda ya aiko min da hotuna na babu sutura a jikina, da wasu kuma a lokacin yana tarawa da ni, sannan ya turo min numbar wayar babana, tare da yi min barazanar zai tura wa mahaifina hotuna da bidiyon da ya dauka na saduwarmu in har ban sake haduwa da shi na biya masa bukatarsa yadda ya ke so ba

 

 

Saboda barazanar da ya yi min, dole na sake komawa inda na bashi dama ya biya bukatarsa son ransa. Bayan ya gama ne, na shiga rokonsa da ya goge hotunan, amma kememe ya ki

 

Bayan na dawo makaranta a Ilorin, nan ma dai ya ci gaba da min barazana cewar lalle na amsa gayyatarsa duk lokacin da ya neme ni ko kuma ya saki bidiyon a yanar gizo

 

Na Shiga damuwa, ga shi kuma na kasa fadawa kowa hatta iyayena saboda za su yi alla-wadai da ni. Daga karshe dai sai na tunkari limamina na coci na fada masa koma tun daga farko har karshe

 

Limamina na Coci ne ya sanar da ‘yan sandan Ilorin da ke jihar Kwara, inda aka yi masa dabara aka saka na gayyace shi zuwa Ilorin, inda a nan ne ‘yan sanda suka kama shi suka karbe wayarsa

 

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Kwara, Ajayi Okasanmi ya tabbatar da lamarin inda ya ce sun kama saurayin amma ya tsere a lokacin da suke kokarin zuwa da shi Otel din ya sauka a Ilorin da samu wasu hujjoji da za su zama shaida

 

Kodayake dai shi wannan saurayi ya je ya rubuta a shafinsa na sada zumunta cewa cin hanci ya baiwa ‘yan sanda suka sake shi ya tsere, amma kakakin ‘yan sanda, Ajayi ya ce in har ya isa ya bayyana kansa ko inda ya ke ko kuma ya fito ya tabbatar da cewa sakinsa ‘yan sanda suka yi bayan sun karbi kudi a hannunsa

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...