Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Kalli Amfani Gawayi Guda 10 Da Ba Ka Taba Sani Ba

Kalli Amfani Gawayi Guda 10 Da Ba Ka Taba Tsammani

0 563

Jama’a da dama musamman a arewacin Nijeriya suna ganin amfanin gawayi bai wuce a saka a cikin dutsen guga ba, ko kuma a cikin kasko domin yin girki ko turaren wuta, ko a dumama daki lokacin sanyi.

Bincike dai ya nuna cewa bayan wadannan alfanun da gawayi ke yi, yana kuma da wasu amfani wajen gyara lafiyar jiki wanda bai kamata mu yi watsi dasu a gidajenmu ba.

Kadan daga cikin amfanin da gawayi ke yi na kamar haka

1) Yana da amfani wajen tsaftace gida da kuma warin jiki misali, idan wani lungu a gida yana wasu, za a iya sanya Gawayi a wurin, in kuwa jiki ne, sai a yi garin gawayin, an sanya a jiki.

2) Gawayi na hana kayan marmari lalacewa, abin da za a yi kawai shi ne a dama gawayin sai a tsoma kayan marmarin a ciki

3) Gawayi na taimakawa wajen cire sinadiran da ke da lahani daga cikin kayan abinci. Za a tsoma kayan marmarin cikin ruwan Gawayi

4) Gawayi na sanya hakora su yi haske idan aka yi amfani da shi wajen goge hakoran.

5) Gawayi na dawo da dandanon miyar da ake tunanin ta lalace, abin yi kawai shi ne a Jefa gutseren gawayin cikin miyar

6) Gawayi na taimakawa wajen rage yanayin lailayi da juya yayin da mutum ya sha nau’ukan magangunan da ke janyo irin wadannan yanayin.

DUBA: Cututtukan Mata Da Maza Da TAFARNUWA Ke Magancewa

7) Gawayi na da amfanin wajen maganin miki ( ciwo) a jikin mutum

8) Ana iya amfani da Gawayi wajen tsaftace gurbataccen ruwan sha

9) Gawayi na maganin Ulcer idan mutum yana cinsa akai akai

10) Ana amfani da Gawayi wajen magance Cututtukan fatar jiki kamar kuraje da rigakafin gurbacewar jiki sakamakon cin wani nau’in abinci.

KARANTA: Hanyoyi 3 Da Kayan Kwalliyan Zamani Ke Haifarwa Fata Mummunan Matsala

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...