Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Kalli Hotunan Tambayoyin Aji 4 Na Firamare Da Malaman Kaduna Suka Kasa Amsawa

0 1,345

Kimanin kaso biyu cikin uku na malaman Firamare a jahar Kaduna ne suka fadi jarrabawar aji hudu da aka basu.

Gwamnan jahar, Nasir El-Rufai shi ya bayyana haka a ranar Litinin da ta gabata yayin da yake karbar bakuncin tawagar bankin Duniya a ofishin sa.

Ya ce malamai 33,000 ne suka dauki jarrabawar, amma a cikin su kaso 66 cikin dari ba su iya cin maki 75 a cikin dari ba.

A don haka ne gwamnan ya ce gwamnatin sa na da niyya sallamar malamai kimanin 20,000 daga ayyukan su tare da daukan wadanda suka cancanta kimanin 25,000 domin su dawo da martabar ilimi a jahar.

Mai karatu zai so ya ga tambayoyin da aka yi wa wadannan malamai da suka kasa amsawa.

Ga su nan a kasa, kamar yadda Jaridar Premium Times ta wallafa:

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...