Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Kalli Kasuwancin Da Wasu Manyan Jaruman Kannywood Ke Yi Banda Harkar Fim

Kalli Kasuwancin Da Wasu Manyan Jaruman Kannywood Ke Yi Banda Harkar Fim

0 698

Akwai manyan jaruman masana’antar Kannywood da dama ba harkar fim kadai suka dogara da shi domin neman na kansu ba, da yawa daga cikinsu na gudanar da wasu harkokin kasuwanci don biyan bukatunsu na yau da kullum.

Wannan na nuna cewa suma dai yan kasuwa ne wanda wasun su ke da shagunan kasuwanci kamar su:

Hadiza Aliyu Gabon

Sananiyyar Jarumar Kannywood Hadiza Gabon tana cikin matan fim din dake kokari wajen nuna kasuwancin ta. Jarumar na da gidan kwalliya da na gyaran gashi mai suna Hadiza Gabon Beauty salon wanda yake titin wharf road dake garin kaduna.

Maryam Booth

Maryam Booth kwararriyar yar kwaliya ce kuma tana harkar siyar da siyarwa irin su kayan sayawa da kayan kwaliya

Maryam Booth kwararriyar yar kwaliya ce wacce kuma ke  harkar siya da siyarwa, tana da shagon da ake yi wa mata kwalliya da siyar da kayan sawa a  birnin Kano mai suna Maryam Booth Beauty Parlour and Collection.

Masoyan Maryam da ma masu bibiyan shafinta a kafafen sada zumunta sun san cewa wannan jarumar ba ta wasa da sana’ar da take yi.

Ita kanta ma ba ta boye aikin da take yi bayan fim. kwararriyar mai kwalliya ce kuma bata boye basirar yi ma mata kwalliya indai har an tuntube ta.

 Rahama Sadau

Ba’a baro fitacciyar jarumar Kannywood da Nollywood Rahama Sadau a baya ba wajen neman na kanta. Kamar dai sauran abokan aikin ta ita ma tana da gidan kwalliya na mata irin ta zamani wanda ke garin Kaduna mai suna Sadau Beauty Lounge.

Bayan haka akwai kamfanin Sadau Pictures wanda ke daukar nauyin shirye-shiryen Fina-finai da nishadantarwa duk cikin abubuwan kasuwanci da take yi. Wannan kasuwancin nata ana iya cewa ya zamanto na iyali domin yan uwanta ke tafiyar da kasuwancin.

Isa A Isa

Isa Abdulkadir Isa

Isa Abdulkadir Isa babban mai shirya fim ne kuma jarumin ya dade yana gudanar da kasuwanci. Shi ya shirya fim din Safara kuma ma’ajin kungiyar yan wasan kwaikwayo na hausa, shine shugaban kamfanin I A I travel agency kamfanin dake daukar dawainiyar masu neman tafiya kasashen waje musamman kasasshen larabawa.

Yana da shagon sayar da kayan sawa irin ta zamani mai suna Queen Nabila Boutique kana shine shugaban kamfanin I A I entertainment and film production wanda ke daukar nauyin shirin fim.

Hassan Giggs

Hassan Giggs yana kasuwancin ruwan sha da lemu

Hassan Giggs Fitaccen Darakta kuma babban mai bada umarni ne a fina-finan Kannywood, yana kasuwancin lemu da ruwan ta gorar roba mai G-Nature

Hassan Giggs shi ya malalki kamfanin ruwan gorar nan ta G-Nature, kamfanin da ta ke kuma sarrafa lemun sha kala-kala.

Ga masu bibiyan shafukan shi zaku shaida cewa Hassan Giggs baya rowan bada ruwan kamfanin shi ga abokan huldar shi har ma da masoyan shi.

 

KARANTA: Taurarin Fina-Finan Hausa Sun Zama Jakadun Jami’ar NOUN

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...