Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

An Kama Wasu Sun Sayi Yaro Dan Shekaru 5 Akan N15,000 a Kano

0 292

Rundunar ‘yan sandan jahar Kano ta cafke wasu ma’aurata daga jahar Rivers da wata ma’aikaciyar asibiti daya a bisa kama su da laifin sayen yaro mai shekaru 5.

An yi cinikin yaron ne dai akan farashin Naira dubu 15 kacal.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Magaji Musa Majiya shi ya bayyana haka ga manema labarai a jiya Laraba.

Ya ce sun samu labari ne daga wajen mahaifiyar yaron da ake so a saya mai suna Hajiya Fatima, inda daga nan ne suka sanyawa mutanen tarko.

Majiya ya ce a lokacin da Haj. Fatima ta fada masu abunda ke faruwa, sai suka ce mata ta yarda za ta sayar da yaron.

KARANTA WANNAN: Mai Dakina na dab da shafa min Kanjamau – Ibrahim Salati

Ya ce mutanen sun daddale da Haj. Fatima cewa za su sayi yaron akan Naira N15,000, inda suka bada 13,000 anan take.

Ya ce sun kama ma’aikaciyar asibitin mai suna Itopam Pious a ranar 10 ga watan nan a yayin da ta ke yunkurin kwace yaron daga wajen mahaifiyar shi da karfin tsiya.

Yayin da ta ke amsa laifin ta, Pious dai ta ce za ta saye yaron ne ta baiwa ma’auratan wanda suka taso takanas takano daga jahar Rivers domin wannan dalili.

A cewar ta, sun shafe shekaru 12 da aure ba su samu haihuwa ba.

Toh sai dai ma’auratan sun musanta aikata wani laifi. Sun ce su fa da takardun su suka zo kuma za su je gidan marayu ne domin a ba su da a bisa doka da ka’ida, kuma ba su san wata hajiya Fatima ba.

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...