Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

“Kana Son Samun Gida (Baini) A Cikin Aljannah ?”

0 355

Abi Malik Al’ash’ari (R.A) yace: Annabi (saw) yana cewa: Lallai a cikin aljanna akwai wani baini wanda ana ganin cikinsa daga wajensa, kuma ana ganin wajensa daga cikinsa (kamar da qarau aka yi shi). Allah ya tanadi wannan baini ne ga masu wadannan soffofi:

 Wanda yake Sassauta magana ( baya cin mutumci).

 Wanda yake ciyar da abinci (ga mabukata).

 Mai kokarin yin azumin nafila.

 Mai yin Sallah da dare a lokacin da mutane suke barci
#صححه الألباني.

Abdillah bn Amru (R.A) yace: Manzon Allah (saw) yace: Lallai a cikin aljanna akwai wani baini wanda ana ganin cikinsa daga wajensa, kuma ana ganin wajensa daga cikinsa, sai Abi Malik Al’ash’ari (R.A) yace: Na wanene wannan Baini ya Manzon Allah? sai Annabi (saw) yace: Na wanda yake dadada magana ga mutane (wato mai kyautata harshen sa). Da wanda yake ciyar da abinci (ga mabukata) kuma yake kwana yana ibada a lokacin da mutane suke barci.
@صححه الألباني.

Allah ka sanya mu aljanna firdausi, amin

Rubutawa: Sheikh Aliyu Said Gamawa (Hafizahullah)

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...