Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Kiwon Lafiya: Ko Kun San Cewa Karo Na Samar Da Waraka Daga Ciwon Koda?

0 956

Cutar koda a wannan zamanin ta zama ruwan dare, saboda Allah kadai yasan yawan mutane da ta yi sanadiyyar ajalinsu, saboda haka ‘yan uwa kuzo mu taimaka mu ceci rayuka daga halaka daga wannan mummunar cuta

 

A jaridar UKAZ da ke garin Palastine an rawaito cewa wani saurayi mai shekaru 35 ya warke daga cutar koda bayan an yi masa wankin koda (dialysis ) na tsawon shekara daya abun bayyi ba, sai sanadiyyar amfani da “Qaro”.  Likitan ya tabbatar masa da cewa ya warke har abada kuma baya bukatar wankin koda nan gaba.

 

Sannan har yanzu an samu wata yarinya mai shekaru ashirin da daya 21 wacce ta samu wannan matsalar ta koda, aka je aka yi mata gwaji a asibiti, Creatinine nata ya hau zuwa 550 amma sai ya ragu ya koma 200 bayan ta yi amfani da karo na tsawon sati uku kacal

Karanta Wannan: Hanyoyin Kula Da Lafiyar Jikinka A Lokacin Hunturu

 

Misalai irin wannan suna da yawa saboda haka ya zama dole ‘yan uwa su yada wannan bayani saboda kowa ya karu.

To ya ya za a yi amfani da shi?

 

Za a nika karon ko a daka sosai har ya yi laushi, daga bisani sai a debi cikin babban cokali biyu da safe a zuba a ruwa kofi daya, sai a barshi kamar sa’a biyu ko uku har ya narke, sai a garwaya sosai a sha da safe kafin, sannan a maimaita haka da yamma sai asha kafin bacci.

KALAR KARON DA ZA KU YI AMFANI DA SHI:

Za ku samu asalin karo na itacen karo wato (Kolkol) da shi ake yin amfani.

Haka za’aci gaba da amfani da shi har a samu sauki domin karo bashi da wata illa kamar sauran magunguna.

 

Daga Mujallar Gaskiya News 24

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...