Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Ku Kalli Bidiyon Yadda Jarumi A Wakar Rap Eminem Ya Caccaki Donald Trump

0 452

Shahararren mawakin rap na kasar Amurka Eminem ya caccaki shugaba kasar Amurka Donald Trump a yayin da ya bayyana shugaban a matsayin babban mai nuna bambancin fata a cikin salon wakensa.

 

Mawaki Eminem ya caccaki shugaba Trump a wani bidiyo da aka fitar a bikin bada lambar yabo ga jarumai a masana’antar nishadantar wa na BET HIP POP AWARD.

 

Bidiyon na da tsawon kusan minti 5 inda mawakin ya yi waken cikin fusace tare da zazafan kalamai don nuna kyama da adawa da shugaban Amurka, Donald Trump ke wa bakaken fata.

 

“Wariyar Launin fata ne kawai abin da ya fi kwarewa akai” in ji Eminem a cikin baitikansa.

 

Sannan mawakin ya ambaci tsohon shugaban Amurka, Barack Obama, a baitikansa inda ya ce ya fi Trump da ke shirin kaddamar da yakin Nukiliya da kasar Koriya ta kudu.

 

Daga karshe Eminem ya yi kira ga magoya bayansa su bijerewa Trump.

 

Ku kalli bidiyon a kasa:

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...