Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Kwallon Kafa: Sanchez Ne Zai Fito Da Kokarin Lukaku Fili – Rooney

0 325

Kamar yadda tsohon dan wasan Man Utd din ya fada cewa Alexis ne zai iya taimakawa Lukaku yayi abinda ake bukata daga gurinsa a Man Utd.

 

Lukaku da Sanchez dai sune suka ciwa Man Utd kwallayensu 2 a nasarar da kungiyar tasamu akan Huddersfield a karshen satin da ya gabata, wanda shine wasan Sanchez na farko a gaban magoya bayan Man Utd a Oltirafod.

 

Kokarin dan wasa Lukaku ya disashe bayan ya fara gasar Firemiya ta bana da Man Utd da ruwan kwallaye amma sai ya zo ya dakushe, Rooney yace dan wasan zai dawo karsashinsa saboda zuwan Sanchez kungiyar.

 

Kamar yadda Rooney ya gayawa gidan TV na Sky sports “A ganina Alexis shine dan wasan da yafi dacewa da Man Utd, yana da kwazo, yana son kwallo, kuma da ganinsa kaga dan wasa mai nasara, saboda haka ina ganin shine irin `yan wasan da Manchester suka rasa, wato `yan wasan da zasu tura Lukaku yayi aikinsa sosai su taimaka masa su bashi `yanci da sarari yaci kwallaye”.

 

“Sanchez ne zaiyi wadannan abubuwa kuma irinsa ne ake bukata a kungiyar kamar dai dan wasa Tevez a lokacinda ya zo kungiyar ta Manchester Utd.

 

“Irinsu `yan wasa ne da suke daga wasu `yan wasan, kaso goma na `yan wasan da suke tare da shi zai taimaka musu ina ganin Sanchez zai yi wannan”.

 

Rooney ya bar kungiyar kwallon kafa ta Man U a karshen kakar wasanni data wuce zuwa Everton inda ya ci kwallaye 11 a wasanni 29 daya buga.

 

Rooney dan shekaru 32 ya bayyana cewa ya fara shirin ajiye takalmansa inda yace “Zanso na shiga harkar koyarwa, domin kwallo kafa ce gaba daya a rayuwata tun dana taso, itace abinda na sani”

 

 

Daga Mujallar TakaLeda.com

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...