Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Kwallon Kafa: United Ta Kori Jami’inta Sakamakon Nuna Kyama Ga ‘Yan Afirka

0 284

 

Kungiyar kwallon kafa ta West Ham United ta sallami daraktan daukar ‘yan wasa na kungiyar bayan an yi zarginsa da kitsa kutungwilar da zai sanya kungiyar ba zata ta sake daukan dan yankin Afrika ba.

 

Daraktan ya turawa wani jami`in sayayyar ‘yan wasa wasikar Emel yana mai gaya masa cewa basa so a kawo musu ‘yan wasa daga yankin Afrika wai don ‘yan Afirkan basu da da’a kuma suna tada hayaniya in ba a saka su a wasa ba.

 

Hukuncin ya biyo bayan wani rahoto da jaridar “Daily Mail” ta yi inda ta Ambato daraktan ya na cewa `yan Afirka suna hada hayaniya idan ba a sasu a wasa ba.

Karanta Wannan: Gulma Da Duminta Daga Duniyar Kwallon Kafa

 

Kungiyar tace kalaman daraktan sun yi muni kuma sun yi cikakken bincike akan maganarsa, kungiyar kuma ta kara da cewa “West Ham bazata laminci kowanne irin musgunawa ba”.

 

A yau Juma`a mai koyarwar kungiyar David Moyes yace wannan al`amari sam bai bata yanayin da `yan wasansa suke cikiba.

“Nayi Magana da wasu daga cikin `yan wasanmu `yan Afrika kuma sun nuna komai lafiya haka kuma sun yi atisaye sosai, suna cike da kwarin gwiwa, a yanzu muna kokari a Firemiya kuma muna so mu dora akan haka” in ji Moyes

 

“Ni dai ban taba ganin wani tsarin sayen `yan wasa mai cutarwa ba a duk kungiyoyin da nayi aiki dasu.

 

Haka itama kungiyar kwararrun `yan wasa ta ce wannan kalamai ya girgizata kamar yadda suka ce “kungiyarmu ta PFA tayi Allah wadai da irin wannan tunani kuma a harkar kwallon kafa wannan tunani bashi da guri”.

 

A cikin `yan wasan West Ham 11 na farko 8 daga ciki `yan Afrika ne wanda suka hada da Cheikhou Kouyate, Pedro Obiang, Joao Mario, Angelo Ogbonna, Arthur Masuaku da kuma Edimilson Fernandes.

 

A watan janairun nan dan wasa Difra Sakho ya bar kungiyar zuwa Rannes, shima Andre Ayew dan kasar Gana ya bar kungiyar zuwa Swansea.

 

 

Madogara: Mujallar TakaLeda

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...