Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Mai Ɗakina Mayyar Raƙashewa ce; Bata Da Aiki Sai Halarta Casu Da Tarayya Da Ƙawayen Banza – Wani Mai Gida Ya Fadawa Kotu

0 399

 

Wani manajan da aka bayyana sunansa da Oluwafemi Ajadi a jiya Litinin ya gurfanar da mai dakinsa a gaban kotun al’adu da ke zamanta a Agege, jihar Legas, inda ya bukaci da kotun ta raba aurensa na shekaru 16 da Chinwe bisa zargin bin maza da ta ke yi da kuma kokarin daukar ransa

 

Amma sai Chinwe mai shekaru 35, cikin hawaye ta roki kotu da kar ta yarda ta raba auren nasu na shekaru 16, inda ta ce ko kafin a daura musu auren, sai da ta zubar da ciki sau da dama wanda shi mijin nata ne ya yi mata

 

Magu Ya Zayyana Sunayen Barayin Kudin Fansho

Ajadi, wanda dan asalin garin Ibadan ne babban birnin jihar Oyo wanda ke zaune a gida mai lamba na 26, kan titin Bamgboye a unguwar Mushin da ke jihar Legas, ya bayyana mai dakinsa a matsayin mace mai jin isa da ji-ji da kai, ga ta kuma iya rigima

 

Ya ci gaba da cewa “Matata ba ta da aiki sai halartar party. Duk inda ta ji da wani taro da za a yi casu, a rakashe, to tana can”

 

“Na yi iya bakin kokarina na raba ta da kawayen banza, amma ta ki jin magana”

 

“Ga bin maza kamar akuya, sannan ga halin ko-in-kula da kuma rashin kimanta darajar aure. Ni dai ina rokon kotu da ta raba aurenmu,” Ajadi ya koka

 

Chinwe ta musanta dukkan zarge-zargen da Ajadi ya shigar akanta tare da rokon kotu da kar ta kashe mata aure

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...