Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Majalisa Za Ta Binciki Buhari Da Jonathan Game Da Abunda Ya Faru Da Biliyan N11.1 Da Aka Warewa Asibitin Aso Rock a Shekaru 3

0 429

Majalisar wakilan Nijeriya ta yanke hukuncin bincikar shugaban kasa Muhammadu Buhari da wanda ya bar masa gado, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan game da abunda ya faru da makudan kudaden da aka warewa asibitin fadar shugaban kasa tsakanin 2015 da 2017 wanda adadin sa ya kai Naira biliyan 11.1.

Majalisar ta kuma yabawa uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari da ta sanarwa duniya abunda asibitin ke ciki.

Diyar shugaban kasa Zahra Buhari da mahaifiyar ta Aisha Buhari dai su suka yi korafi akan yadda ko sirinji  babu a sibitin ballantana magungunan da za a yi amfani da su wajen kulawa da marasa lafiya.

Dan majalisa mai wakiltar Akwa Ibom, Henry Archibong shi ya gabatar da kudirin binciken a gaban majalisar, wanda kuma majalisar ta amince da shi.

Yayin da ya ke gabatar da kudirin, dan majalisar ya bayyana yadda a kowacce shekara ake warewa asibitin makudan kudade domin ya gudanar da ayyukan shi yadda ya kamata.

Ya ce a shekarar 2015 asibiti ya samu biliyan 3.94, a 2016 ya samu 3.87 sai kuma a 2017 da asibitin ya samu biliyan 3.2 wanda gaba daya kudin ya kai naira billiyan 11.1 a cikin wadannan shekaru.

A cikin wadannan shekaru uku, gaba daya asibitocin gwamnatin tarayya guda 16 da ke fadin kasar nan abunda suka samu dan kaso ne kadan idan aka kwatanta da abunda asibitin Aso Rock ya samu shi kadai.

KARANTA WANNAN: Jami’an tsaro sun samu muggan makamai a gidan Nnamdi Kanu

Ya ce a 2015 asibitocin gwamnatin tarayyan 16 sun samu biliyan 1.424, a 2016 sun samu biliyan 3.333 sai a 2017 da suka samu biliyan 1.943.

Dan majalisar ya ce indai irin wannan badakala za ta iya faruwa a karkashin hancin shugaban kasar, me ake tsammanin ya ke faruwa a wasu guraren.

A cewar shi ” Wannan abun kunya ne ga kasar nan. Ba za mu yarda da shi ba”

“Ba za mu yar da cewa duk da wannan badakala, babban sakataren gwamnatin tarayya da ministan lafiya ba su yi murabus ba”

A don haka ne majalisar ta kafa kwamiti na musamman da zai yi bincike akan batun da kuma zargin ana ragewa ma’aikatan asibitin albashin su.

Kwamitin zai gabatar da binciken shi nan da makonni uku.

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...