Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Masu Daukan Hoto Guda 9 Da Suka Fi Shahara a Arewacin Nijeriya

0 379

Wadannan masu daukan hoto su muka fi ganin sunayen su musamman a bukukuwan manya da masu fada a ji a Arewacin Nijeriya:

1.Mai Gaskiya: Sunan shi Abdul-Uthman mai gaskiya kuma ya zama sananne ne kimani shekaru 5 da suka gabata. Mai gaskiya shi ne mai daukan hoton sarkin Kano Muhammad Sanusi na II kuma shi ya dauki hotunan auren diyar shi, Fulani Siddikat.

2. George Okoro: Duk da cewa inyamuri ne, ya yi suna sosai a fannin daukan hoto a Arewacin kasar nan, musamman a Abuja ina ya ke aiki. Ya koyi daukan hoto a garin New York da ke kasar Amurka kuma ya dauki hotunan auren manya da dama a kasar nan.

3. Atilary Studio: Sunan shi na gaskiya Alex kuma shi ma dan Abuja ne. Ya dauki hotunan bukukuwa sama da 500 a fadin Nijeriya a ciki har da na dan gidan tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ibrahim Mantu da Amaryar shi ‘yar gidan biloniyan nan dan jahar Benin, Cif Lucky Igbinedion.

4. Eye of Insanity Photography: Sunan mai shi Abdul Qudus wanda dan asalin jahar Kogi ne amma ya na aikin shi a Abuja. Shi ma ya yi suna a fannin daukan hoto a Arewacin Nijeriya. Adbul Qudus shi ya dauki hotunan auren dan tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dakta Musa Babayo.

5. Ahmedzol: Ahmed Abdullahi ya yi suna a jahar Bauchi a fanni daukan hoto. Shi ya dauki hoton auren dan tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Nabeel Ahmed Yayale da na tsohon gwamnan jahar Bauchi.

6. Libature Photography: Mai wannan gidan daukan hoto shi ne mamallakin Arewa Magazine da Mirror Online inda ya ke wallafa hotunan da labaran auren manya.

KARANTA WANNAN: Aisha Buhari ta bukaci matan Arewa su tashi tsaye domin neman ilimin boko

7. Deenee Photography: Nuruddeen Mohammad ya yi suna ne a jahar Sokoto inda ya kasance zabin manyan da masu fada a ji a jahar.

8. Stevereinz: Shi kuwa a jahar Kaduna ya yi suna. Shi ne mai daukan hoton jarumar Kannywood da Nollywood, Rahama Sadau.

9. Maikatanga: Sani mai Katanga shi ma ya yi suna a Arewacin Nijeriya, inda ake wallafa wasu daga cikin hotunan shi a jaridar Daily Trust. Ko a shekarar 2016, Maikatanga shi ya dauki hotunan auren diyar Kanal Sani Bello, wanda tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar ya hallarta.

Fassara daga wata makala da aka wallafa a jaridar City People Online

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...