Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Mata Mu Hankalta: Yadda Na Cinnawa Kaina Wuta Don Na Ji Mijina Na Waya da Wata Mace

Ina Kira Ga Mata Da Kar Wacce Ta Kuskura Ta Gwada Rashin Nazarin Da Na Aikata.. Sam ban yi tunani ba

0 1,013

 

Wata mace ‘yar shekaru 35 ta bayyana nadamarta bisa yadda ta cinnawa kanta wuta, sanadin da ya sa ta samu mummunan raunin kuna kawai wai don ta kama mijinta yana cin amanar aurenta da wata mace

 

Matar da aka bayyana sunanta da Felicia Mokeka ‘yar asalinkasar Afirka ta kudu ta ja hankalin mata da cewa babu namijin da ya kamata a ce wata mace ta kashe kanta ko raunata kanta a kansa, kamar yadda matar ta fadawa jaridar Daily Sun

 

A watan Yunin bana ne, Felicia ta yi kanta wanka da ruwan sipirit, inda ta cinnawa kanta wuta da ba don mijin nata ya yi hanzarin kashe wutar daga jikinta ba, da tuni ta sheka barzahu

 

Felicia ta ce, Ubangiji ya bar ni da raina ne don na zamto darasi ga sauran mata don su guji ko kaucewa tabka irin kuskuren da ta tabka

Yadda lamarin ya faru shi ne: Wata rana na dawo gida daga aiki kafin lokacin da na saba dawowa, kuma da ya ke mijinta kan rigata dawowa gida daga inda ya ke aiki, sai na shiga cikin gidan na rufe ko’ina kamar dai ban dawo ba don na yi wa mijina ba zata

 

Ko da ta ji mijinta na bude kofa, a lokacin da ya dawo daga aiki, sai ta buya a bayan doguwar kujera da nufin ta bashi tsoro in ya shigo gidan

 

Amma kawai sai ta ji yana waya da wata mace cikin shauki da soyayya, da ya ke ya bar sifikar wayar a bude, sai ta ji matar da ya ke wayar da ita na tambayar mijin nata cewa, “Ina matarka Felicia?”

 

Bude bakin mijin nata sai cewa, “Au, wannan. Tana can wurin aikinta ko kuma tana kan hanyar dawowa. Koma dai a ina ta ke a halin yanzu ni bai dame ni ba. Ta je can ta karata”

 

Felicia ta ce, daga nan mijina da budurwarsa suka ci gaba da fadin munanan abubuwa a kaina babu kakkautawa kamar ba wanda muke kwana mu tashi a kan gado daya ba. Kuma kamar ba shi ne uban ‘ya’yana biyu da na haifa masa ba

 

 

Yana kashe wayar, bayan da ya fadawa budurwa tasa na kusa dawowa gida, sai kawai na dago daga bayan kujerar da na buya. Kawai ya ganni a bayansa. Nan take ya rikece ya gigice

 

Nan take na nufi dakina na fara tattara ya nawa-ya nawa zan bar masa gidansa. Ina cikin hada kayana ne kawai sai na hangi kwalbar sifirit (wanda dama na san yana cin wuta). Kawai sai na dauka na antaya shi a jikina sannan na kyattawa kaina ashana

 

Ba don mijina ya zo ya kashe wutar ba wacce ta dan dauki lokaci tana cin jikina da ba yanzu labari ya sha bambam

 

 

Na sami mummunar kuna a jikina, inda sai da na shafe watanni biyu a asibiti kafin na sallame

 

 

Zuwa yanzu dai na samu lafiya kuma ina iya aiwatar da komai da kaina. Sai dai ina mai baiwa  mata shawara da cewa kar wata ta taba kokarin halaka kanta don mijinta ya kyamaceta.

 

 

Da zarar kin fahimci cewa aurenki baya tafiya daidai, ma’ana hankalin mijinki baya tare da ke ya koma wajen wata, shawarata ita ce ki tattara ki bar masa gidansa

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...