Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Mata Ta Zubawa Mijinta Tafasasshen Ruwan Zafi (Hoto)

0 124

‘Yan sanda sun cafke wata mata wadda ta watsawa mijinta tafasasshen ruwan zafi a jikinsa a kan wani dan rashin fahimtar juna da suka samu.

 

Karanta wannan: Wata Ta Kashe Dan Kishiyarta Mai Shekaru 2 Da Ruwan Zafi a Katsina

 

Wannan abun dai ya faru ne a garin Rubochi wanda ke karkashi karamar hukumar Kuje a ranar Litinin 4 ga watan Disamba 2017.

 

Karanta wannan: Wata Mace Ta Kashe Jaririn Kishiyarta Dan Kwana 40 Da Haihuwa Ta Hanyar Shayar Da Shi Gubar Bera

 

Matan wacce ake kira da suna, Ruth Musa, ta zubawa mijinta, Musa Emmanuel, tafasasshen ruwan zafi bayan sun samu wani dan rashin fahimta a tsakanin su a kan wanda zai taya daya daga ‘ya’yan su neman safar zuwa makarantar sa da ya bata.

 

 

Musa Emmanuel

Karanta wannan: Wata Mata Ta Kashe Kanta Saboda Mijinta Zai Yi Mata Kishiya

 

Emmanuel a yayin da ya ke magana da kafafen yada labarai na City News a gadon asibitin Rubochi ( Rubochi General Hospital) a ranar Talata, ya ce sun dan samu wani dan matsala ne tsakaninsa da matarsa a kan wanda zai taya daya daga dan su neman safarsa na zuwa makarantar da ya bata a safiyar ranar Litinin.

 

Karanta wannan: Uwargida Ta Tura Kanwar Miji Cikin Tukunyar Tafasashen Ruwa Zafi

 

Ya ce bayan an gama yiwa yaran na sa 2 wanka tare da shirya su zuwa makaranta, daya daga cikin su ya fara kuka a kan bai ga safarsa na makaranta ba, karawa da cewa matar na sa ta fadawa dan na su ya je ya duba da kan sa

 

Karanta wannan: Dalilin Da Yasa Matata Ta Soke Ni Da Kwalba – Bilyaminun Zamfara

 

“Kawai na fada mata me yasa ba za ta iya taya shi neman safar ba tunda na yi masu wanka. Da fadin haka kawai sai ta fara zagi na, ni ma na mayar mata da martani

 

Karanta wannan: An Kuma! Wata Mace A Jihar Zamfara Ta Dabawa Mijinta Kwalba A Kahon Zuciya (Hotuna)

 

“A yayin da mu ke musayar kalamai, kafin na ankara, ta dauke sauran tafasasshen ruwan zafin da ta daura bisa kan wuta.

 

Karanta wannan: Shari’ar Biyaminu Da Maryam Zama Na 1: Kotu Ta Umarci Da A Garkame Maryam Har Zuwa Ranar Da Za Ta Ci Gaba Da Sauraren Karar

 

Mijin wanda aka watsawa ruwan zafin, dan shekaru 42, ya kasance makarantar sakandare na gwamnatin tarayya da ke yankin ne wato Federal Government College Rubochi.

 

Karanta wannan: Bilyaminu Ya Cancanci Hukuncin Da Maryam Ta Yi Masa -Inji Wata Kawar Maryam

 

Mijin ya ce saboda tsananin zafin da ya ji, sai da ya fadi kasa, inda ya ce makwabtan su suka taimaka wajen garzayawa da shi asibiti

 

Karanta wannan: Gaskiya Ta Bayyana: ‘Yan Sanda Sun Samu Bidiyon Abinda Ya Faru a Yayin Kisan Bilyaminu Bello

 

Musa dan asalin Jaba ne a jihar Kaduna sannan kuma yana da yara 2, ‘yan shekaru 5 da 3.

 

Karanta wannan: Sababbin Bayanai Game Da Kisan Bilya Da Maryam Sanda Ta Yi Daga Shaidar Gani Da Ido

 

A yayin da manema labarai suka tuntubi hedikwatan ‘yan sanda na yankin Rubochi, shugaban ‘yan sanda na yankin, CSP John Kareem, ya tabbatar da faruwan hakan inda ya ce ‘yan sanda sun cafke matan tare da kargame a kurkuku sannan kuma suna gudunar da bincike a kan lamarin.

 

Karanta wannan: Bakin Kishi: Miji Ya Dabawa Matar Shi Wuka Sau 40

 

“Hakika, mun cafke matan da ta aikata wannan mummunar abu tare da kargame ta a dakin kurkukun ‘yan sanda, a yayin da mu ke gudunar da bincike a kan lamarin,” inji shi.

 

Karanta wannan: Wata Ta Kashe Dan Kishiyarta Mai Shekaru 2 Da Ruwan Zafi a Katsina

 

Kafafen yada labarai na City News ta samu labarin cewa abu irin haka ya faru a garin Toto da ke kusa da Abaji a jihar Nasarawa a ranar Asabar da ta gabata, a yayin da wata mata aure, Fatima, ta watsawa kishiyarta tafasasshen ruwan zafi. A yanzu haka matar da ta aikata wannan mummunar abu ta tsare ba a san inda ta ke ba, amma har yanzu ‘yan sanda na neman suna neman ta don su cafke ta.

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...