Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Matsalolin Rashawa Da Cin Hanci Da Hanyoyin Magance Su- Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa

0 642

GABATARWA
Wannan maudu’I yana da matukar muhimmanci musamman a wannan lokaci da sabuwar gwamnatin Nigeria ta Shugaba Muhammadu Buhari ta saka yaki da rashawa da cin hanci a cikin manyan abubuwan da gwamnati za ta sa a gaba. Za mu duba mana’anar rashawa da cin hanci, da matsayinsa a cikin al’ummu daban daban, da nau’ukansa, da abubuwan da suke janyo shi da wadanda suka fi tafka rashawa, da matsalolin da su ke biyo baya, sannan mu duba matakan da suka kamata a dauka don samun mafita.

 

MA’ANA
Rashawa itace saba ka’ida, ko doka, ko nuna rashin yakamata wajen wanda wani iko yake hannunsa; haka kuma za ta iya daukar ma’anar barna ko ta’adi, musamman a cikin dukiya. A harshen larabci ta na nufin fasadi; a yaren turanci ta na nufin corruption.

Cin hanci nau’I ne na rashawa wanda ya ke nufin bayar da wani abu, kamar kudi ko kadara, ga wani wanda iko ya ke hanunsa domin ya kauda kai game da wani abu da aka aikata, ko ake shirin aikatawa, ba bisa ka’ida ba.

MATSAYIN RASHAWA A CIKIN AL’UMMU DABAN DABAN:Rashawa ko barna da dukiyar jama’a ta na da mummunan matsayi a cikin kowace irin al’umma.

Misali, a tarihin Yahudawa idan aka samu mutum da laifin rashawa, ana yi masa hukuncin da suke kira excommunication, watau yankewar alaka. Tsarin ya tanadi gabatar da mutum a dakin ibada a cikin duhun dare, an kunna kyandura a dakin. Bayan kowa ya halarta sai a zaunar da mutum a tsakiyar mutane, a bushe duk kyanduran, sai jagora ya karanta addu’ar yanke alaka da mai laifin, mutane su na cewa amin. A cikin addu’ar ana cewa Ubangiji ya jefa mailaifin a cikin duhun da yafi wanda ake ciki a dakin, a roke Ubangiji ya la’ance shi cikin dare da rana, a ambaci duk wani nau’I na bala’I, a yi fatan ya fada masa, albarkacin littatafansu masu tsarki da babukansu guda dari shida da talatin; a umarci mutane da su yanke duk wata alaka da mailaifin, ace kada kowa ya aura daga gareshi kada a aurar masa, kada ayi magana da shi, kada a rubuta masa wani sako, kada a karanta abinda ya rubuta; a karshe kuma a raka shi iyakar kasa ya bar garin.

A tarihin Yarabawa, idan aka samu Alafin da laifin rashawa, ana shirya buki ne kowa ya taru a wani dandali, sai Bashorun ya karanta masa laifinsa, daga nan sai a bukaci ya sha dafi ya fadi ya mutu.

A kasar China, har izuwa yau, wanda aka samu da laifin rashawa ana kashe shi ne ta hanyar harbi da bindiga, kuma iyalai ko danginsa su za su biya kudin harsashin da za a kashe shi da shi. Shigen haka abin ya ke a makwabtan China, irinsu Japan, da Taiwan, da Korea, da Hongkong.

Musulunci ya zo da kakkarfan hani ga rashawa da cin hanci ko barna da dukiyar jama’a, sannan ya ayyana horan da za a yi idan an samu mutum da laifin hakan. Idan aka bibiyi kissar Annabi Shu’aibu, Alaihissalam, kamar yadda ta zo a suratu Hud (Q11:84 – 93) da suratul A’araf (Q7:85-96) za a ga rukunin abubuwa biyu aka yi umarni da su, kuma aka yi hani da rukunin abubuwa biyu:

(i) umarnin kadaita Allah da bauta, kada a yi shirka da Shi;

(ii) umarnin a cika mudu, kada a tauye shi, ko a hatsi ne, ko a kayan miya, ko yadi, ko duk wani abin da ake aunawa da mudu ko sikeli, ko lokacin zuwa aiki da tashi;

(iii) hani ga dukkan nau’I na barna, kamar rashawa da cin hanci, ko almundahana, ko satar dukiyar gwamnati, ko fashi da makami, ko cin riba, da makamantansu; sai

(iv) hani ga tare hanya ana tsoratar da mutane, kamar yadda ake kuka da ‘yan sandan Njeriya, da ‘yan Roadsafety, da VIO da ‘yan KAROTA, da makamantansu (an fi so su tsaya daga inda za a hango su, a kaucewa laifi, ba su labe a kwana ba don su yi kamu).

Bugu da kari Qur’ani yazo da hani ga rashawa da cin hanci a suratul Baqara:

”kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku da karya, kuma ku sadar da ita ga mahakunta domin ku ci wani yanki daga dukiyoyin mutane da zunubi, alhali kuwa ku, kun sani.” (Q2:188)

Mutanen Annabi Shu’aibu ba su yarda da risalarsa ba. Hasali ma cewa suka yi:

”Ya Shu’aibu, yanzu sallar ka ce ta ke umartarka da (ka sa) mu bar abin da iyayenmu suke bauta wa, kada kuma mu aikata abin da muka ga dama da dukiyoyinmu? Hakika kaine sarkin hakuri shiryayye!” (Q11:87).

(Za mu cigaba, da yardar Allah)

 

Daga: Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...