Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Matsalolin Rashawa Kashi Na Biyu- Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa

0 350

Hukuncin da ya biyo bayan mutanen Annabi Shu’aibu, da suka ki bin umarnin Annabinsu, shine tsawa da ta saukar musu, suka wayi gari a guggurfane a cikin gidajensu, kamar ba su taba zama cikinsu ba (Q11:94-95); sannan a karshen kissar a suratul A’araf aka ce:

 

”da dai mutanen alqarya sun bada gaskiya sun kuma ji (tsoron Allah), to ba shakka da mun bude musu (kowadanne hanyoyi na) albarka daga sama da kasa, amman kuma sun karyata (ayoyinmu), saboda haka sai Muka kama su domin abin da suka zamanto suna aikatawa.”(Q7:96).

 

Amman hukunci mai dorewa, game da rashawa ko fasadi, yana cikin suratul Ma’ida:

 

”saboda wannan Muka hukunta a kan Bani-isra’ila cewa duk wanda ya kashe wani mutum ba da (laifin kisan) kai ba, ko kuma wata barna a bayan kasa (kamar kafurci ko fashi ko rashawa) ba, to kamar ya kashe mutane ne gaba daya, wanda kuma ya raya shi to kamar ya raya mutane ne gaba daya. Hakika Manzanninmu sun zo musu da (ayoyinmu) mabayyana, sannan hakika yawancinsu, bayan wannan ma, masu barna ne.” Q5:32)

sai aya ta gaba ta ce:

 

”ba wani abu ba ne sakamakon wadanda su ke yiwa (Musulmi masu bin) Allah da ManzonSa fashi kuma suke tafiya a bayan kasa da barna ba, sai kawai a kashe su ko kuma a tsire su ko a yanke hannayensu da kafafuwansu a tarnake ko kuma a kore su daga kasar. (Yin) wancan kaskanci ne a gare su a duniya; a lahira kuma suna da azaba mai girma.” (Q5:33)

Sannan ga hadisin Abu-Huraira wanda Manzon Allah (SAW) ya
ce : Allah ya la’anci mai bada cin hanci da mai karba.

 

NAU’O’IN RASHAWA:

Rashawa ko barna da dukiya ta na da nau’uka daban daban, daga mafi kankanta zuwa ga manya manya. Wannan kuwa sun hada da anfani da kananan kayan ofis, ba akan ka’ida ba (kamar su takardu, da file jacket, da envelops da makamantansu); ko yin anfani da manyan kayan ofis, su ma ba bisa ka’ida ba (kamar motoci, ko wasu kayan aiki, ko na’urori); haka kuma yin aikin da ba a amince da shi ba a lokacin da ya ke na ofis ne; ko yin amfani da ma’aikatan ofis domin zuwa su yiwa shugaba wata hidima ta kashin kansa a lokacin ofis.

 

Haka kuma nau’I ne na rashawa karbar kudi a hannun dalibai da nufin basu sakamakon jarrabawa wanda ba su cancanta ba; ko neman yin lalata da mace kafin a bata sakamakon jarrabawa, ko daukarta a aiki ko yi mata promotion ko posting din da ya dace da ita.

 

Sai karbar cin hanci daga wanda ake zargi da wani laifi, ko da nufin yi masa wani aiki ko bashi wani hakki wanda ya ke nasa ne; ko kashe-mu-raba da dukiyar gwamnati, kamar a samma wa masu karbar haraji wani abu daga cikin harajin, ita kuma hukuma a bata kadan ko a hana ta baki daya.

 

Akwai kuma nau’I na sama-da-fadi da dukiyar gwamnati, kamar yadda ake zargin gwamnatin tarayyar Nigeria da ta gabata ta yi wajen wawure dollar million ashirin ($20m)[kimanin N4’400b) na dukiyar man fetur; akwai ma wasu kudaden makamantan haka da ake zargin an yi sama-da-fadi da su. Haka kuma kwanannan gwamnoni suka koka da cewar ba su san inda kudin rarar man fetur ya shiga ba, wanda a shekarar 2010 ya kai dollar million dubu goma da million uku ($10.3b), amman a wannan shekarar ta 2015 kudin ya rikito zuwa dollar million dubu biyu da million shida ($2.6b) kuma ba tare da an raba an baiwa kowace jiha kasanta ba! Ko ina gwamnatin Jonathan ta kai kudin? Oho!!!

 

Wasu manyan ma’aikatan gwamnati sukan hada baki da manyan kanfanonin kasashen waje wajen satar man fetur, ko kwangen biyan fetur din da aka fitar da shi, ko yiwa gwamnatin kasa yankan baya game da duk wata dukiya da ya kamata ta shigo mata, ko ta kin biyan harajin da ya dace.
(Za mu cigaba, da yardar Allah)

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...