Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Matsayin Mace A Musulunci: Mace ‘Yar Gata – Farfesa Aliyu A. Jibia

0 461

Hakika addinin Musulunci ya yiwa mace kyakkyawan tanadi kuma ya ba ta matsayin da ba wani tsari na Dan Adam (komai kyawunsa) da ya kwatanta irinsa tsawon tarihi. A wajen Ibada, Ubangiji Madaukakin Sarki ya raba lada daidai wa daida a kan ko wane jinsi, namiji ko mace. Amma saboda raunin mace, Allah bai kallafa ma ta nauyi ba illa nauyin kula da mijinta da reno da kuma tarbiyyar yara. Saboda wahalar da ta ke tattare da rayuwa, Ubangiji ya kallafa nauyin mace marhala marhala akan ba’arin majibintanta. Misali, yayinda aka haifeta, tana karkashin kulawar iyayenta har zuwa lokacin aurenta. A yayinda ta yi aure tana karkashin kulawar mijinta. Idan ta haihu kuma ta manyanta a shekaru, tana karkashin kulawar ‘ya’yanta da mijinta idan Allah yayi masa jinkirin kwana. Idan har ba ta da kowa, to tana karkashin kulawar hukuma da al’ummar Musulmi.

 

Idan mu ka lura sai mu gane cewa babu wani lokaci a rayuwar mace da aka dora ma ta nauyin kula da kanta. Hasalima, Annabi Mai tsira da aminci ya tabbatar cewa, aljannar ta tana karkashin kafar mahaifiyarsa, watau kyautatawa uwa yana daga abinda zai arzuta bawa da gidan aljanna.

 

A gefe guda kuma, ingantattun hadisai sun nuna cewa tun daga ranar da mace ta dauki ciki har zuwa ranar da ta yi arba’in bayan ta haife, idan ajali ya zo mata, ta yi shahada. Wannan ba karamar daraja bace da Allah Madaukakin Sarki ya ba ‘ya mace. Wannan gatanci da matsayi ya kai matuka.

 

A karshe, nasihar da Annabi SAW yayi a hajjin bankwana ta dada tabbatar da wannan gatanci da kula, a inda Annabi SAW ya fada sau uku, “Na horeku da ku ji tsoron Allah ku kiyaye haqqin mata”. Allah ya sa iyayenmu mata su kula da wannan gatancin su rike amanar mazajensu, amin. Wallahu Aala

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...