Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Miji Ya Watsawa Uwargidansa Tafasasshen Ruwa Zafi A Fuska

Miji Ya Watsawa Uwargidansa Tafasasshen Ruwa Zafi A Fuska

0 292

‘Yan sanda reshen jihar Borno sun cafke wani maigida, Bukar Ali, a kan zargin watsawa matarsa na farko wato uwargidansa, Falmata Bukar, ruwan zafi a fuska.

 

Kwamishinan ‘yan sanda reshen jihar Borno, Damian Chukwu, ya tabbatarwa manema labarai a kan faruwan hakan inda ya ce wanda ake zargi na hannun ‘yan sanda a birnin Maiduguri.

Karanta wannan: Sirikina Ne Ya Cancanta Ya Gaje Ni – Gwamna Okorocha

Chukwu ya ce an cafke Ali ne a 3 ga watan Fabrairu a unguwar Shuwari II da ke birnin Maiduguri, bayan ya aikata mummunar aikin.

 

“Wanda ake zargi ya kasance mai mata 2 ne, sannan kuma wani dan matsala a shiga tsakaninsa da uwargidansa wacce ke shayar da jariri dan watanni 7.

Karanta wannan: Wani Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Zai Tsaya Takarar Shugaban Kasa a 2019

 

“A yayin da ta ke girka abinci karya kumallo, shi wanda ake zargi ya watsa ma ta ruwan zafi a fuska, sakamakon hakan ya sa ya ji ma ta rauni,” ya ce.

 

Kwamishinan ya ce matan da aka jiwa rauni an garzaya da ita zuwa asibitin Maiduguri wato Specialist Hospital, Maiduguri, inda ya kara da cewa ‘yan sanda sun fara gudunar da bincike a kan lamarin.

 

Karanta wannan: Wani Dan Nijeriya Ya Yi Alkawarin Biyan Duk Wanda Ya Yi Rajistar Zabe Wasu Adadin Kudade

 

Ali, duk da haka, ya fadawa manema labarai cewa wai yana kokarin amshe ruwa zafin ne daga hannun Falmata sai ya watsa ma ta shi a fuska ba tare da sanin shi ba.

 

Ya ce, “Ta watsa ma ni ruwan zafi ne, shine ni ke kokarin hana ta watsa ma ni kuma, a yayin da ne ke kokarin amshe ruwa zafin ne daga hannun Falmata sai ya watsa ma ta shi a fuska.

Karanta wannan: Dubban Jama’a Sun Sauya Sheka Daga Jam’iyyar PDP Zuwa APC A Kwara

 

“Mun kasance ma’aurata na tsawon shekaru 8 sannan kuma Allah ya ba mu ‘ya’ya 4 tare, ba da son rai na ba ne na aikata wannan mummunar aikin.”

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...