Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Mijina Bashi Da Tarbiyya; Yana Dukana, Ya Sadu Da Ni A Gaban ‘Ya’yanmu – Wata Mace Ta Fadawa Kotu

0 3,091

Wani direban keke mai kafa uku da aka fi sani a arewacin Nijeriya da A Daidata Sahu ya rasa aurensa na shekaru 17 bayan da mai dakinsa ta kai shi kara kotu bisa abinda ta kira cin zarafi, rashin tarbiyya da rashin mutunci a gareta

 

Matar da aka bayyana sunanta da Bolanle ta fadawa kotu cewa “Babu rashin mutuncin da ya fi mijnki, uban ‘ya’yanki a matsayin mace ya sadu da ke a kan idon ‘ya’yan naku”

 

 

Bolanle ta ci gaba da cewa “Mai gidana, Olasunkanmi, na da dabi’ar cin zarafina musamman ma in ya yi sha. Ya kan dawo ya bukaci ya sadu da ni a gaban ‘ya’yanmu, amma da na yi kokarin na nusar da shi illar “abin da ya ke kokarin yi, sai ya kama ni da bugu sannan ya sadu da ni ta karfin tsiya a gaban ‘ya’yan namu suna kallo muna tarawa kiri-kiri”

 

 

“Akwai ranar da na dawo daga aiki na tarar da yaranmu daya akan daya, suna kwatanta abinda suke ganin muna yi ni da mahaifinsu” Bolanle ta fada cikin takaici

 

Sai dai, shi Olasunkanmi ya roki kotu da kar ta raba aurensa da matarsa duk kuwa da bai musanta zargin da ta ke yi masa na cewa yana saduwa da ita a gaban yaransu ba

 

Olasunkanmi ya ce “Ina rokon kotu da kar ta raba aurena da mai dakina domin ina kaunarta har yanzu. Na san na yi kuskure, amma a shirye nake da na gyara kura-kurai na

 

A lokacin da ya ke zartar da hukunci, babban alkalin kotun al’adu da ke zamanta a unguwar Igando, jihar Legas, Mai sharia Moses Akinniyi ya zartar da cewa kotu ta raba aure tsakanin Olasunkanmi Abdul-Kareem da Bolanle Abdul-Kareem

 

Mai Shari’a Akinniyi ya ce, duk da tsawatarwa da shiga tsakani da kotu ta yi da kuma ‘yan uwa, amma Olasunkanmi ya ki ya sauya halinsa

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...