Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

MOBO Awards: Shugaba Buhari Ya Yabawa Wizkid Da Davido

0 89

Shugaba Muhammadu Buhari yabawa Ayodeji Balogun, wanda aka fi sani da suna WizKid, da kuma David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, a kan samun lamabar yabo na mawakan bakaken fa watao MOBO.

 

Karanta wannan: Abunda Shugaba Buhari Ya Ce Game Da Sayar Da ‘Yan Nijeriya Da Ake Yi a Matsayin Bayi a Libya

 

Buhari ya ce mawakin biyu na nuna cewa lallai akwai ‘yan Nijeriya da suke da baiwa a harkar waka, inda ya ce sun kasance abun alfahari ga kasar ta aiyukar su da wakokin su.

 

Karanta wannan: Shugaba Buhari Ya Tafi Kasar Jordan Don Halartar Zama A Kan Matsalolin Tsaro

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a wani sanarwa da ya fitar ta mai bai shi shawara na musamman a kan harkokin da suka shafi yada labarai da hulda da jama’a, Femi Adesina.

 

Karanta wannan: Dalilin Da Yasa Shugaba Buhari Ba Zai Taba Ganawa Da Maina Ba – Itse Sagay

 

A sanarwan, “Shugaba Buhari tare da masoyar mayakan na gida da waje suna taya mawakan murna a kan samun lambar yabon.”

 

Karanta wannan: Tinubu Ya Sanar Da Ni Abubuwan Da Ban Taba Sani ba – Shugaba Buhari

 

Shugaban kasan ya tabbatar da cewa mawakan 2 sun nuna irin baiwan da Allah ya ba ‘yan kasar, sannan kuma sun kasance abun alfahari ga kasar ta wakokin su,” a yayin da ya yaba da kwazon su, tare da irin gudunmawa da suke yi.

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...