Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Mutane Da Dama Sun Rasa Rayukansu A Rikicin ‘Yan Sanda Da Masu Hakar Ma’adanai

0 786

Mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon barkewar rikici a tsakanin masu hakar ma’adanai ba a bisa ka’ida ba da ‘yan sanda a fili hakar albarkatun kasa da ke yankin Mayo Sine wanda ke bisa tsaunin Mambilla, a jihar Taraba.

 

Karanta wannan: Barazanar Kai Hare Abuja Dagaske Ne – Inji ‘Yan Sanda

 

Rahotanni daga kafafen yada labarai na DailyTrust ta gano cewa abun ya faru ne a yammacin jiya, a yayin da wasu tawagar jami’an tsaro na ‘yan sanda suka kai wata barazanar hare zuwa filin da ake hakar ma’adanai don kora su mutanen da ke gudunar da aiki a filin ba a bisa ka’ida ba amma masu hakar gwal din suka ki bin umurnin hukumar.

 

Karanta wannan: ‘Yan Sanda Sun Kama Wasu ‘Yan Fashi Da Makami A Gombe

 

An sake gano cewa masu hakar ma’adanai a wannan filin sun kai sama da 10,500 inda yawancinsu sun kasance ba asalin ‘yan kasan Nijeriya ba ne, sannan kuma sun dade suna gudunar da aiyukar hakar ma’adanai ba a bisa ka’ida ba na tsawon shekaru 10.

 

Karanta wannan: Rikicin Mambilla: Jami’an Tsaro Sun Gano Kabarurruka Makil Da Gawawwakin Fulani (Hoto)

 

Kafafen yada labarai na Daily trust ta gano cewa dan isar tawagar ‘yan sanda da aka aika zuwa wurin don kora masu hakar ma’adanai a filin, sun rusawa masu hakar gine-ginen su da ke wurin tare da amshe kayayyakin da suke amfani da su wajen hakar kasa.

 

Karanta wannan: Dan sanda Ya Kashe Dalibar Kwaleji Kan Cin Hancin N200

 

An kora masu gudunar da aiyukan hakar ma’adanai ba a bisa ka’ida ba don gwamnata ta ba wata kamfanin harkar ma’adanai mai zaman kanta filin, amma sun ki su bar filin, hakan ya sa aka aika jami’an tsaro na ‘yan sanda don su kora su.

 

Karanta wannan: Kaico!!! Ta Kashe Kawunta A Yayin Da Ya Nemi Yin Lalata Da Ita

 

Abunda wai jami’an tsaro na ‘yan sanda da aka aika kora su daga filin suka yiwa masu hakar ma’adanai din ya sa suka fusata, ya sa masu hakar suka kora ‘yan sandan tare da cinnawa kayayyakin aikin kamfanin hakar  ma’adanan da gwamnati ta ba filin wuta.

 

Karanta wannan: Rikicin Taraba: An Bukaci Gwamnati Ta Hanzarta Tura Jami’an Soji Zuwa Mambila

 

Wani mijiya da ke wurin a lokacin da abun ya faru, ya fadawa manema labarai da cewa a yayin da ‘yan sanda ke kokarin kora masu hakan ne suka bude masu wuta, inda suka kashe mutanen da dama tare da jikkata wadansu da dama daga cikinsu.

 

Karanta wannan: ‘Yan Sanda Sun Bankawa Matatun Man Fetur 40 Wuta A Edo

 

A yayin da aka neme karin haske daga jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda reshen jihar Taraba, DSP David Misal, ya ce bai da wata masaniya game da lamarin.

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...