Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Mutane Na Siyar Da Yara Kamar Yadda Ake Siyar Da Gyada A Jahar Kaduna – Haj. Hafsat

0 332

Kwamishinan harkokin mata na jahar Kaduna, Hajiya Hafsat Mohammed Bala ta bayyana cewa safarar kananan yara na dada karuwa a fadin jahar, a inda ta ce mutane na cinikin kananan yara kamar yadda ake siyar da gyada a jahar

Kwamishinan ta bayyana hakan a yayin da ta ke ganawa da manema labarai bayan ma’aikatan mata na jahar ta samu ceto yara 37 wadanda aka niyyar siyar da su.

“Muna fama da safarar kananan yara da ake yi don mutane a yanzu suna siyar da kananan yara kamar yadda ke siyar da man gyada,” Kwamishinan ta ce.

Karanta wannan: ‘Malaman Jahar Kaduna 21,780 Suka Fadi Jarabawar ‘Yan Aji 4 Na Firamare’ – El- Rufai

“A kwanakin baya da suka gabata, an yiwa wata karamar yarinya fyade wadda ta sanadiyyar ta rasa rayukan ta a jahar. Yara kanana da dama suna rasa rayukan su ta harkar lalata da ake yi da su? A kowane lokaci, wannan mummunar abun yana kalubalantar iyaye maza da mata,  wakilan su, da malamai, da kuma makamancin su. Ba za  tsaya mu yi shiru ba, mu rinka ganin irin wannan abu na faruwa ba musamman ma yadda ake cin zarafin kananan yara,” Ta ce.

Haj. Hafsat ta ce gwamnatin jahar Kaduna tana iya kokarin ta a wajen ganin ta kawo karshen irin wannan mummunar abu da ke faruwa a jahar inda ya bayyana cewa ma’aikatan kiwon lafiya, da hukumomin SEMA da NEMA tare da jami’an tsaro na ‘yan sanda sun hada wani katuntumi a kan safarar kananan yara da ke jahar ke fama da shi.

Karanta wannan: Likitoci Sun Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani A Jihar Kaduna

“Muna bukatar mutane su hada kai da Gwamnati sannan kuma iyayye sun zanto masu kulawa da harkokin  yaran su a ko da yaushe,” Ta ce.

Madogara: Linda Ikeji Blog

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...