Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Na Shiga Fashi Da Makami Ne Saboda Na Biya Sadakin Matata – Inji Wani Dan Fashi

0 206

Wani dan fashi da ‘yan sanda suka cafke ya ce ya shiga harkar ne domin ya samu Naira N300,000 da zai biya kudin sadakin matarsa.

Dan fashin mai suna Chukwuma Okoro ya fadawa manema labarai a jiya Laraba a garin Akure da ke jahar Ondo cewa iyayen matar ne suka yanke masa wadannan kudade.

Okoro wanda ya ce bai taba sata ba, ya ce ganyayyaki ya ke sayarwa a Akure kuma shi babu ta yadda zai samu wadannan kudade, a don haka ne ya fara nema ido rufe.

KARANTA WANNAN: Evans ya yi yunkurin tserewa daga hannun ‘yan sanda

Mai magana da yawun ‘yan sanan jahar, Femi Joseph ya ce sun samu bindiga daya da alburusai guda biyar a hannun Okoro.

Ya ce sun kama Okoro ne bayan da ya bi wata mai sayar da kayayyaki mai suna Chinenye. A lokacin ta na dauke da N550,000 da za ta kai banki.

Okoro dai ya yi yunkurin karbe kudaden da karfin tsiya kafin ya fadi daga kan mashin din da ya ke kai, mutanen gari suka damke shi.

Jami’in ya ce nan ba da dadewa ba za su gurfananr da Okoro a gaban kuliya.

 

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...