Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Nagarta 5 Da Shugaba Buhari Ya Rasa A Matsayinsa Na Jagora – Tanko Yakasai

0 318

Tsohon dan majalisar wakilan Nijeriya a zamanin Shehu Shagari, Alhaji Tanko Yakasai ya zargi al’ummar Nijeriya da yin kunnen uwar shegu da jan kunnen da ya yi ta yi musu na kar su zabi Buharin kafin zaben 2015, inda ya bayyana cewa ya yi ta yin wannan kashedi ne sakamakon masaniya da ya ke da ita na cewa Buhari bashi da wasu nagarta har guda biyar da shugabanci ke bukata

“Shekaru na 92 yanzu, in har ban yi amfani da nazari, hikima, fasaha da gogewata ba yanzu, to, sai yaushe zan yi amfani da su?”

“A lokacin da na bayyanawa ‘yan Nijeriya ko wane ne Buhari, na sha kalubale ta sama da kasa, hagu da dama musamman ma daga wannan yanki namu na arewa. Daga wancan lokaci ne na yanke hukuncin bari na yi shiru bayan gamsuwa da na yi cewa watan wata rana ‘yan Nijeriya za su fahimci abinda nake nufi”

Karanta: Zaben 2019:  Buhari Na Cikin Hatsari –  Junaidu Muhammad

“Ni a ganina kowane kyakkyawan jagoranci na bukatar wadannan muhimman abubuwa biyar da suka hada da: Gogewa, iya gudanar da aiki, hangen nesa, kyakkyawa shiri/tsari, sai kuma gaskiya da rikon amana”

“A ra’ayina, wannan gwamnatin ta rasu wadannan nagarta gaba dayansu duk kuwa da kasancewarsu suke tuka shugaba zuwa ga mulkin adalci. A yanzu dai babu yadda muka iya da yanayin da muka tsinci kanmu a ciki, dole mu hakura mu ci gaba da zama a wannan yanayi har zuwa wa’adin wannan gwamnati,”

inji Tanko Yakasai

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...