Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Ni Gawurtaccen Mai Busa Sigari Ne; Amma ban Taba Dandana Barasa Ba – Shugaba Muhammadu Buhari

0 2,564

A wata tattaunawa da ya yi jaridar Sun da ya yi a baya-bayan nan, Shugaba Muhammadu Buhari ya fadi bayyanawa jaridar wasu bayanan sirri game da kansa

 

Ko da jaridar ta tambayeshi, ya fada mata wasu abubuwa da ya yi a baya amma yanzu ya bar yinsu, sai Shugaba Buhari ya ce:

 

“A da ni gawurtaccen mai busa sigari ne, amma na daina shan sigari tun a shekarar 1977”

Shugaba Buhari ya ci gaba da cewa “Ban taba dandana giya ba a rayuwata”

“Ko a lokacin da na ke soja, akwai wannan al’adar ta shan giya a lokacin kaddamar da kai a matsayin cikakken soja, amma sai na ce musu, hukumar soja ta baiwa kowa damar dabbaka addininsa iya iyawarsa, kuma ni addinina ya hana shan giya. A saboda haka sai aka mutunta bukatata aka kyale ni ban shan giyar ba.”

 

“A saboda haka babu wani lokaci da aka taba tilasta ni na sha giya a matsayina na soja, kuma nima ban taba shan giya bisa radin kaina ba saboda ina da bukatar na kasance a cikin hankalina a koda yaushe ”

 

“Masu ta’ammali da giya sun ce in har ka sha kwalba daya, to, za ka so ka kara wata kwalbar, daga nan kuma sai ka shiga tanbele”

 

“Ya kuma kamata a ce mata suna ra’ayina, amma wani abin mamaki, sai ya kasance ban dada su da kasa ba. Watakila akwai wani abu a tattare da ni da basa so”

 

“Ina mai tabbatar maka da cewa,ban taba shan giya ba, na taba shan sigari kuma na yi ‘yan mata kawaye”

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...