Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

PDP Ta Caccaki Shugaba Buhari Kan Yunkurin Ciwo Bashin Dala Biliyan 5.5

0 276

Jam’iyyar Adawa ta PDP ta caccaki yunkurin shugaba Buhari na ciwo bashin dala biliyan 5.5 daga kasasshen waje.

Wannan ya biyo bayan sanarwan da kakakin jam’iyyar PDP Dayo Adeyeye ya fitar a jiya Laraba a birnin Abuja.

Sanarwan ta bayyana rashin amfanin ciwo bashin makudan kudade har dala biliyan 5.5 inda ta ce karbo bashin kudade irin wannan zai kara jefa kasar cikin bashi, tare da jefa goben kasar cikin halin kaka naka yi.

PDP ta ce, a matsayinta na jam’iyyar da ta mulki kasa na tsawon shekaru 16, ta damkawa jam’iyyar APC mulkin dake kumshe da lafiyayyen tattalin arziki a 2015, dole ta bayyana takaicinta game da yadda lamurra ke cigaba da tabarbarewa a kasa.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...