Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

PDP Ta Zargi APC Da Kokarin Gurbata Taron Da Za Ta Gudanar Ranar Asabar

0 196

Premium Times ta rawaito cewa Jam’iyyar  PDP ta zargi jam’iyya mai mulki ta APC da kokarin gurbata babban taron da jam’iyyar ke shirin gudanarwa a ranar Asabar mai zuwa

 

Jam’iyyar PDP ta bayyana wannan zargi ta bakin sakataren yada labarai na jam’iyyar Dayo Adeyeye inda ta ce, APC na shirya makirci don rushe babban taron da jam’iyyar ke kokarin gudanarwa a ranar Asabar, 9 ga watan Disamba.

 

PDP ta ce,  akwai wasu jami’an gwamnatin Buhari dake shirin hargitsa babban taron da zata gudanar sannan kuma tana kira ga shugaban kasa da ya shigo lamarin sannan kuma ya dakatar da su.

 

Haka zalika, Shugaban kungiyar amintattu na PDP, Walid Jibrin, yace jam’iyyar na duba zuwa ga tarban shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso da kuma wasu gwamnonin da suka bar PDP a shekarar 2014 zuwa ga jam’iyyar PDP.

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...