Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Sake Fasalin Kasa Ko Fasalin Halayyar Jama’ar Kasa – Dahiru Suleiman Dutse

0 376

Sake fasalin kasa dai kalma ce wacce ta fito daga bakin tsohon Shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ( murabus) a sakonsa na goron Sallar bana a bisa hasashen lalubo masalaha ga batutuwan sukurkucewar alamuran kasa da ta zamantakewar jamaarta. Duk da kasancewar a dunkule Janar din ya furta wancan kalami, amma da dama sun fi zaton hanzarinsa ba zai wuci ta neman a yi wa tsarin turakun madafun iko kwaskwarima ba.

 

Amma dai a ragewa madafun ikon tarayya karfi a kirkiro tsarin lardi-lardi domin kara musu karfi ta wajen gudanar da alamuran kasa shigen fasalin zaman kasar a da kafin bullo da tsarin gwamnatocin tarayya, jihohi da kuma majalisun kananan hukumomi. Acewar Na Maryam mai ki fadi ta bullo da wannan matakin gudanar da salon shugabanci ne kadai za a sami maganta warware matsalolin bangaranci da sukurkucewar tsarin rabon tattalin arzikin kasa da kyautatuwar muamalar yau da kullum ga wadanda ake shugabanci domin su maana jamaar tarayyar Nijeriya.

 

Karanta wannan: Zaben 2019: Tazarcen Gwamna Badaru Tana Kasa Tana Dabo – Dahiru Suleiman Dutse

 

Abin nufi anan shi ne a bai wa kowannae lardi ikon cin gashin kansa tare da sarraf albarkatunsa ga masu albarkatun kasa, su kuma wadanda ke kanfar albarkatun kasa ko oho, ka ga anan akwai sauran rina a kaba ke nan, wanda hasashen masana ke ganin a maimakon a sami maslaha babu abin da wannan tsari zai wanzar face rudu da karin rigingimun bangaranci wanda kwamacalar hakan ke iya jefa kasar fuskantar karin matsaloli a maimakon daidaituwar alamura kamar yadda ake da zummar shimfidawa.

 

Amma kuma a tsokacinsa a game da wannan batu, an saurari tsohon Shugaban kasa Janar Olushegun Obasanjo da fadin cewa ba sake fasalin kasa Nijeriya ke bukata ba a yanzu illa sake fasalin tarbiyyar jamaar kasa. Babban dalilinsa anan shi ne ba za ka ambaci batun kishin kasa ba muddin jamaar kasa ba su da daar kishin kasarsu ko kishin kansu da kansu. Sanin kowa ne dai babu abin da ke jawo mana nakasu a kasar nan face rashin kishin kanmu ballantana kasar haihuwarmu, ba don komi ba sai don son zuciya da kin aiki da gaskiya akan dukkan alamuranmu na yau da kullum.

 

Saboda haka muddin muna son kasarmu ta kara bunkasa tare da ci gaba sai fa lalle mun rungumi kyawawan dabiun kishin kanmu da kanmu gami da cusa wa kanmu kishin kasarmu ta hanyar rungumar aiki tukuru da sadaukarwa tare da sanya tsoron Allah a zuci gami da rungumar halayyar gaskiya da aiki da gaskiya a duk inda muka sami kanmu.

 

Ya zama wajibi mu yi watsi da dabiu marasa kyau kamar hainci, karya da son zuciya da lalaci, a maimakon haka mu rika kasancewa cikin kyawawan dabiun daa da tsoron Allah da kaunar juna da rungumar aiki tukuru domin amfanin kanmu da kanmu ko kasarmu Nijeriya za ta ci gaba kamar sauran kasashe da ke doron kasa.

 

Shi ma a nasa shrhin, Shugaban kasarmu na yanzu wato Janar Muhammadu Buhari cewa ya yi babu babban abin da ya fi dacewa da mu a yanzu illa mu kaunaci Allah da gaskiya tare da rungumar aiki tukuru domin kishin kasarmu kana da jan damarar taimakawa kasa da kyawawan adduoi da sadaukarwa ta hakika ta haka ne za mu yantar da kanmu da kuma kasarmu Nijeriya amma ba daurewa soki burutsu gindi ba da cewa hakan babu inda zai kaimu face yin nadama da koma baya.

 

Idan muka waiwayi baya kuwa za mu ga ai Marigayi Malam Aminu Kano ma ya taba ankarar da wakilan majalisar tsara kundin tsarin mulkin Nijeriya cewar wajibi ne mu yi laakari da abubuwa guda biyar muddin muna son mu yi nasara ga wannan muhimmin nauyi da aka aza mana. Wadannan abubuwa kuwa sun kunshi lalle mu tsaida tsoron Allah a zukatanmu a yayin gudanar da wannan zama na shata kyakkyawar makoma ga kanmu da kuma kasarmu Nijeriya.

 

Sauran sun hada da mu cire son kai da son zuciya, illa mu dubi Allah akan dukkan shawarwarin da za mu gabatar masu karbuwa ne, kuma sun dace da yanayinmu da kuma aladunmu. Na ukunsu wajibi ne mu amince shigar da tsarin zamantakewarmu da kuma aladunmu a cikin wannan kundi na tsarin mulki, kana kuma mu Musulmi a ba mu damar shigowa da tsarin shariar Islama haka suma abokanen zamanmu Kristoci su ma mu amince su shigo da tsarin addininsu na Kristanci ta yadda dukkan mabiya addinan guda biyu kowa in ya yi laifi a rika yi masa hukunci da karantarwar addininsa, alamarin da Malamin ya sha suka kakkausa akai na cewar Nijeriya ba kasar da take bin tafarkin addini daya ba ce, alamarin da ya fusata Marigayi Malam Aminu da cewa matukar ba mu daidaita alkiblarmu akan wadannan shawarwari biyar ba, la burda ba za mu yi wa juna adalci ba, da cewar ina mai fargabar taron nan namu kada ya zama taron yan shan shayi wanda ba zai haifar mana da komai ba face rudu da hayaniya.

 

A don haka a iya cewa tun farko kin bin aiki da shawarin manya na a zauna a tsara zaman tare a bisa kyakkyawar fandisho shi ne ummul habaisin rikita rikitar kasar nan wanda hakan ya samo asali daga munafunce- munafuncen alummomin kasa da wakilansu a dalilan son zuciya da kwadayin abin duniya, alamarin da a iya cewa shi ya dabaibayemu muka kasa gaba, muka kasa baya.

 

Idan ba haka ba yaushe za a ce yau shekaru hamsin da bakwai da samun yancin kanmu amma har yanzu a kullum batu ake ta ruwan sha bai wadacemu ba, asibitocinmu na kanfar rashin magunguna a asibitico da kwararrun likitoci,babu kyakkyawar yanayin aiki ga maaikata balllantana albashin kirki, illa sata da yawaitar cin hanci da rashawa. Zuciyoyinmu sun mace mu ke nan sai yawan maula mun gaza sarrafa komai, komai kawomana ake daga waje, duk da kirarin da ake mana na uwar garke a Afirka, amma ba mu da komai kuma ba ma iya sarrafa komai, alhali kananan kasashen da muka yi musu zarra da ba su kai rabin-rabinmu ba sun yi mana fintinkau a ta fannoni da dama, a dalilin halayyar kishin kansu da ta kasarsu gami da rungumar akidar yin aiki tukuru domin ci gaban kasar haihuwarsu sabanin mu da muka rungumi akidar cima zaune.

 

Karanta wannan: Shekaru Biyu Da Mulkin APC: Nasara Ko Koma Baya? – Dahiru Suleiman Dutse

 

Ko da dai an dauko hanya ta amsa kiran Shugaban kasa kan a koma gona. Alhamdullahi koma gonar da aka yi a bana a gaskiya an ga faidarsa tunda ko ba komi an sami yalwar abinci, da fatan za a ci gaba. Ita kuma hukuma ta kara rungumar harkar noma da muhimanci ta wajen kula da bunkasa matakansa kamar bangaren samar da wadataccem takin zamani akan kari a kuma farashi mai rangwami ga manoma ba da iri irin na zamani da bayar da dabarun noma ga manoma akai-akai, kana da bai wa manoma wadataccen tallafin bunkasa aikin gona ta hanyar samun rancen kudin noma da garmuna da magungunan feshi da na kwari da makamantansu a wadace, kuma a kowanne lungu da sako sako na kasar nan.

 

Saboda haka lokaci ya yi da za mu yi wa kanmu kiyamullaili wajen yaki da zukatanmu ta wajen gyara zuciyoyinmu da rungumar kyawawan dabiun daa da tsoron Allah a alamuranmu na yau da kullum, da aiki tukuru domin ci gaban kanmu da kasarmu Nijeriya ba don komi ba sai don kare mutuncinmu da ta kasar haihuwarmu da ba mu da kamarta a duk fadin duniyar nan. Muna kira ga Shugaban kasa Janar Buhari da ya dubi sake maido da shirin nan na yaki da rashin daa da ya taba bullowa da shi a yayin shugabancin kasa cikin kakin Soja da cewa wannan shirin ya taimaka matuka wajen sake fasalin halayyar k yan kasa da kyautata zamantakewarsu, muddin muna son mu farfado da kanmu da kuma kasarmu daga turbar rugujewa.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...