Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

An Sako Jarumin FinaFinan Hausa Da Masu Garkuwa Suka Sace A Abuja

0 980

A daren Lahadi ne masu garkuwa da mutane suka sace sannanen jarumin finafinan Hausa Al’amin Buhari bayan ya taso daga Abuja zuwa garin Jos.

Rahotan da muke samu a yanzu haka ya bayyana cewa masu garkuwan sun saki Jarumin bayan da aka biya diyyar naira Dubu 500

Wani abokinsa wanda yasamu zantawa da shi ta wayar tarho ya tabbatar da cewa Al’amin yana nan da rai, cikin koshin lafiya kuma zai koma wajen iyalinsa dake garin Jos.

Furodusan finanan Hausan nan mai suna, Usman Mu’azu ya tabbatarwa da cewa a halin yanzu jarumin yana Abuja, kuma ana sa ran gobe Laraba zai tafi Jos.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...