Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

SALATUL MAKRUB (Sallar Yayewar Damuwa)- Daga Zauren Fiqhu

0 1,234

Hadisi daga Hasanul Basariy daga Sayyiduna Anas bn Malik (ra) yace:

 

“Akwai wani mutum daga cikin Sahabban Manzon Allah (saww) daga cikin Al-Ansar (Mutanen Madeenah) ana kiransa da suna “ABU MU’ALLAQ” (ra). Ya kasance shi Attajiri ne yana yin kasuwanci da dukiyarsa da kuma ta mutane.

 

Yana zuwa garuruwa daban-daban. Ya kasance shi mutum ne mai yawan ibadah kuma mai yawan tsantseni (kyamar haram).

 

Wata rana ya fita domin kasuwancinsa sai ya hadu da wani ‘Dan fashi wanda yasha ‘damara da makamai kala-kala a jikinsa. Sai ‘dan fashin yace masa “Ajiye dukkan abinda ke tare dakai domin ni kasheka zanyi”.

 

Sai yace masa “Mai yasa kake son zubda jinina alhali ga dukiyar nan kaje kayi sha’aninka da ita?”.

 

Sai ‘dan fashin yace “Amma dukiya kam zata zama tawa. Amma ni dai babu abinda nake sai zubda jininka”.

 

Sai Abu Mu’allaq (ra) yace “To tunda ka Qi sai ka kasheni, amma ina so ka kyaleni inyi sallah raka’a hudu”.

 

Sai ‘Dan fashin yace “Sallaci duk abinda kaso”. (Amma dai sai na kasheka).

 

Sai Sahabin nan (Abu Mu’allaq) yayi alwala ya sallaci raka’a hudu. Yana daga cikin addu’o’in da yayi acikin sujadarsa ta raka’ar karshe yana cewa:

 

“يا ودود يا ذاالعرش المجيد يا فعال لما يريد ، أسألك بعزك الذي لا يرام وملكك الذي لا يضام وبنورك الذي ملأ أركان عرشك أن تكفيني شر هذا اللص، يا مغيث أغثني، يا مغيث أغثني ، يا مغيث أغثني.”

 

“Ya Wadood Ya Dhal ‘Arshil Majeed, Ya Fa’alun Lima Yureed! As’aluka bi-izzikal ladhee la yuraamu, Wa Mulkikal ladhee la yudhaamu, Wa bi nurikal ladhee mala’a arkaana ‘arshika, an takfiyanee sharra hadhal Lissi.

 

Ya Mugheethu agithnee, Ya Mugheethu agithnee, Ya Mugheethu agithnee”.

 

“Ya Wadood Ya Ma’abocin Al’arshi mai girma, Ya mai aikata abinda yai nufi, ina rokonka don Buwayar nan taka wacce ba’a samu, da Mulkin nan naka wanda (acikinsa) ba’a zalunci, Kuma don Hasken nan naka wanda ya cika rukunan Al’arshinka.

 

(Ina rokonka) Ka isar min daga sharrin wannan ‘dan fashin. Ya Mai kawo ‘dauki, ka kawo min ‘dauki. Ya Mai kawo ‘dauki, ka kawo min ‘dauki. Ya mai kawo ‘dauki ka kawo min ‘dauki!”.

 

Yayi wannan addu’ar har sau uku. Sai ya hangi wani Mutum akan doki ya taho aguje. A hannunsa akwai wani mashi, ya ‘dora akan goshin dokinsa.

 

Yayin da ‘dan fashin nan ya hangeshi a tafe, sai shima ya taho wajensa. Suna haduwa sai ya soke ‘dan fashin nan da mashinsa. Nan take ya kasheshi.

 

Sannan ya juyo wajen Sahabin nan yace masa “Tashi”.

 

Sai Sahabin yace masa “Mahaifina da Mahaifiyata fansa ne a gareka! Shin wane ne kai? Gashi Allah ya taimakeni da kai”.

 

Sai mutumin yace masa “Ni Mala’ika ne daga cikin Mala’ikun sama ta-hudu. Yayin da kayi addu’ar nan da farko sai naji Kofofin sammai sunyi wata irin Qara!.

 

Sannan kayi addu’ar nan karo na biyu sai naji Mala’ikun sammai sunyi wani irin gunji.

 

Sannan kayi addu’ar nan a karo na uku sai naji ance lallai wannan addu’ar wani wanda ke cikin damuwa ne. Don haka sai na roki Allah yayi min izini in jibinci kisan wannan ‘dan fashin”.

 

Sayyiduna Anas bn Malik (ra) yace “Kayi sani cewa duk wanda yayi alwala yayi sallah raka’a hudu sannan yayi wannan addu’ar, lallai za’a amsa masa. Ko yana cikin damuwa ne, ko ba acikin damuwa yake ba”.

 

– Amma idan kai zakayi akan wata bukatarka, zaka cire daidai wajen “An takfiyanee sharra hadhal Lissi” din nan. Sai ka fadi bukatunka awajen sannan kace “Ya Mugheethu agithnee” sau uku.

 

Don Qarin bayani aduba :

 

– MUJABUD DA’AWATI na Ibnu Abid dunya (shafi na 8).

 

– ‘UYUNUL HIKAYAT na Ibnul Jawzee (shafi na 97-98).

 

– HAWATIFUL JINAAN (shafi na 13).

 

BAYANI

 

‘Yan uwa ku sani cewa Zauren Fiqhu yana kawowa irin wadannan fa’idodin ne domin amfanar da al’ummah. Kuma ita hikima kayan mumini ce. Duk inda ya tsinceta dauka yakeyi.

 

Shi kuwa Munafuki babu abinda ke zuciyarsa sai kiyayya, sai kokwanto, da kuma karya da zantuka marassa tushe.

 

Kuma irin wadannan fa’idodin suna rataye ne da yaqeeni. Wato yarda da cewa Allah zai biya bukatarka mutukar kayi tare da gaskatawa, ba tare da kokwanto ba.

 

Duk addu’ar da kayi acikin kokwanto ba zaka ga biyan bukata ba. Don haka sai a kula.

 

Kuma yana daga cikin ladubban yin addu’a, ka fara da salatin Manzon Allah (saww), sannan kuma ka rufe dashi.

 

Akwai wasu mutane wadanda da zarar sun ga mun rubuto wani abu na fa’idah, ko kuma wata Mu’ujizah ta Manzon Allah (saww) sai su rika bugo waya don neman jayayya dani.

 

Duk abinda nakeyi ina bada reference kaje ka duba. Don haka in jayayya kake so, sai kaje kayi da marubutan littafin ba dani ba..

 

Amma duk wanda zai bugo waya don neman karin haske ko tambaya, wadannan muna maraba dasu. Allah yasa mu dace.

 

DAGA ZAUREN FIQHU (30-12-2016)

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...