Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

An Sallamo Yusuf Buhari Daga Asibiti

0 233

Dailypost ta rawaito cewa an sallamo yaron shugaba Buhari, Yusuf Buhari daga asibitin Cedarcrest a yau bayan jinyar da ya yi sakamakon hatsarin babur a Abuja.

Mataimakin shugaba Buhari na musamman kan kafafin sada zumunta, Bashir Ahmad ya tabbatar da samun saukin Yusuf tare da sallamo shi daga asibitin Cedarcrest.

A ranar 26 ga watan Disamba ne aka kwantar da Yusuf Buhari biyo bayan hatsarin babur daya rutsa da shi a Abuja, bayan nan ne aka farfado da shi babban asibitin Cedarcrest inda aka yi masa tiyata, kuma a yanzu haka ya samu sauki sosai har an sallamo shi daga asibitin.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...