Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Saurayi Ya Maka Bazawara Da Mahaifinta A Kotu, Bayan Sun Ci Masa Naira 710,000 Tare Da Hana Shi Aurenta

0 636

Wani saurayi mai suna Yusuf Mamuda ya gurfanar da wani dattijo mai suna Inusa Aliyu, da ‘yar sa, Jamila a gaban wata kotu a jihar Nasarawa bisa zargin cin amanarsa da cutarsa kudi har naira dubu 710,000 da sunan za a bashi aure.

Frank Swem, Dan sanda da ya gabatar da karar ya bayyana cewa, Yusuf Mamuda ya shigar da kara ofishinsu dake Masaka cewa, wani mutum mai suna Haruna ya hada baki da mahaifin Jamila suka damfare shi kudi naira dubu 650,000 da sunan zasu bashi auren Jamila wacce bazawara ce.

Mahmuda ya ce, Haruna da mahaifin Jamila sun karbi kudinsa ne da sunan kyautar aure kuma sun zambace shi saboda sun san yana neman matar da zai aura

Ya ce “Asirin su ya tonu ne bayan da na fara bincike domin gudun yin aure a cikin aure tunda Jamila bazawara ce, na bukaci a bani shaidar mutuwar aurenta amma sai suka fara yi min wasa da hankali kafin daga bisani suka bukaci na kara bayar da N60,000 domin su je Zamfara su kawo min shaida.”

Dan sanda mai gabatar da karar dai ya shaidawa kotu cewa, Mamuda ya basu adadin kudin da suka bukata amma duk da haka sun gaza kawo masa shaidar mutuwar auren Jamila kafin daga bisani ita Jamilan da kanta ta fada masa cewar tun farko ba ta da niyyar aurensa kuma da bakinta ta fada masa cewar duk abinda ya faru hadin baki ne tsakanin mahaifinta da Haruna domin kawai su damfare shi.

Mahaifin Jamila da Haruna sun musanta aikata laifin inda Alkalin kotun, Yakubu Ishaku, ya amince da bayar da belinsu akan kudi N500,000 kowanne mutum tare da wani na kusa da su da zai tsaya masu, Haka kazalika ya daga sauraron karar ya zuwa ranar 19 ga wata.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...