Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Shanun Buhari Sun Fi ‘Yan Nijeriya Koshi – Inji Mai Taimakawa Wani Gwamna

0 606

Wani mai taimakawa gwamnan jahar Akwa Ibom, Nyesom Wike mai suna Essien Ndueso ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da baiwa shanun shi kulawa fiye da yadda ya ke baiwa ‘yan Nijeriya.

A wani sako da Essien ya wallafa a shafin sa na Facebook a jiya Alhamis dauke da hoton shugaban a gonar shi, ya bayyana cewa mutanen Nijeriya na ta fama da matsalar man fetur da matsin rayuwa amma Buhari ya fi mayarda da hankali akan shanun shi.

Ya ce ana sayar da litar man fetur akan Naira 170 a cikin jahar shi ta Akwa Ibom a maimakon Naira 145 da gwamnati ta kayyade kuma har da wadanda ake biyan su bautawa Buhari a shafukan sada zumunta suna shan wahala.

A cewar shi “Allah ya kawo mu zamanin wani mulki da shanu suka fi mutane koshi”

Ya kara da cewa, “Idan da ace farashin ciyawa zai karu ko kuma aka takura wadannan shanu ta kowacce siga, ina tabbatar da cewa Buhari zai dau mataki cikin gaggawa”

KARANTA WANNAN: Hotuna: Shugaba Buhari ya ziyarci gonar shi a Daura

Sai dai wani magoyin bayan Buhari a jahar. Imaobong Akpan ya mayar da martani cewa babu gwamnatin da ta baiwa jin dadin jama’a muhimmanci kamar ta Buhari.

Ya ce gwamnatin ba ta yin kasa a gwiwa wajen sakin kudade a lokacin da ya kamata domin ta kula da walwalar jama’a.

Ya kara da cewa ya tabbata hauhawan farashin mai da wahalar shi da ake fama da shi aikin ‘yan zagon kasa ne masu hana ruwa gudu.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...