Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Shaye-Shaye Tsakanin Matasa, Daga Ina Matsalar Ta Ke? – Buhari Abba

0 324

Matsalar Safara da shaye- shayen miyagun kwayoyi matsala ce da ke mayar da hannun agogo baya a kokarin da ake na tsabtace halayyar al’umma. Babban abin damuwa a yau shi ne yanda matsalar ta samu gindin zama a tsakanin matasa inda matasa suka tsunduma kansu cikin harkokin shaye-shaye.

 

Hakika dabi’ar shaye-shaye mummunar dabi’ace musamman tsakanin matasa wadan da ake ganin su ne manyan gobe, matasan da idan lokaci ya yi ko hali ya kama su ne zasu jagoranci wannan kasa domin kaita ga gaci. Wannan babbar matsalace da ta ke barazana ga zama lafiyar kowace irin al’umma. Domin wajibin hukumomi ne tsarewa al’ummarsu hankalinsu da lafiyarsu, musamman acikin wannan mawuyacin lokaci.

 

Masu lura da al’amura dai na ganin har su  kansu yan siyasar zamani na taimakawa ga lalata matasa ta fannin shaye-shaye, domin cimma bukatarsu ta kaiwa ga lashe zabe.

 

Karanta wannan: Illar Shaye-shaye Ga Matasa Da Mata

 

Shaye Shaye ya dauki wani sabon salo ta yadda bawai kawai ga maza ya tsaya ba abin har da mata, ta yadda suke shan kwayoyi masu yawa domin su bugu, akwai magunguna da aka sani na tarine ko na mura sai mutum ya yi ta afasu yana korawa da ruwa tun yana gane mutane har sai ya dena, zakaji mamaki idan kaji yadda matasa suke baiwa wannan mummunan aiki muhimmanci, kuma wani Karin abin bakinciki da takaici har da manyan mutane da matsakaitan matasa da kuma dimbin yara sabbin balaga a wannan harka.

 

Magungunan da ake sha domin a bugu sun hada da Benelin da Totalin da emzolin da Rocci da sauran dangogin maganin tari ko mura, irin maganin da ake zubawa acikin ‘yar karamar kwalba ake sha da dan karamin cokali sai ka samu yaro ko yarinya sun daddakeshi a lokaci guda, wanda wannan ya wuce over dose ya tafi alamar hauka, domin maganin da likita zai rubuta da za’ayi akalla mako biyu ana sha amma mutum ya shanyeshi a lokaci guda, wannan hauka ne ko hankali? Wannan ya saba da duk wani lafiyayyan hankali.

 

Galibi yanzu masu irin wannan shan magani domin buguwa mata sukafi yawan yinsa, wasu sukance idan aka hadashi da lemon lakasera ya fi tafiya dai-dai. Shaye-shaye babban laifi ne da ya sabawa hankali da tunanin dan adam, haka kuma ya saba da dokokin kowace irin kasa, kuma ya sabawa addini da al’ada da tarbiyyarmu da zamantakewarmu, lallai wannan babban laifine da ya shafi bangarori da daman gaske, kama daga su kansu masu shaye- shayen da iyaye da al’umma da kuma gwamnati.

 

Karanta wannan: Yadda Wasu ‘Yan Sanda Ke Kwalewa Tare Da ‘Yan Shaye-shaye

 

Iyaye suna da laifi babban akan wannan batu. Domin wasu da yawa suna sane da cewa ‘ya ‘yansu na shaye-shaye amma kuma basa daukar wani mataki na magance hakan, lallai wajibin iyayene su tashi tsaye haikan wajen ganin sun yaki wannan mugunyar dabi’a ta shaye-shaye.

 

Haka kuma, ya zama wajibi ga hukumomi su tashi tsaye domin yaki da sha da fataucin wadan nan miyagun kwayoyi, ta hanyar yin hukunci mai tsanani ga duka wanda aka kama yana harkar safarar wadan nan miyagun kwayoyi da kuma masu sha, lallai dole gwamnati ta takawa ‘yan siyasa birki domin suna taka muhimmiyar rawa wajen jefa ‘yan uwanmu matasa cikin wannan mummunan yanayi, da yawansu su ne suke saya musu wadannan kayan maye, da basu makamai domin su farwa abokan ‘yan hamayya a lokacin zabe ko wani gangami na siyasa. Su kuma a bangaren Matasa ya kamata mu sani cewa babu wata al’umma da za ta yi nasara har a santa a duniya matukar babu saitin kwakwalwa. Nagarta dai ita ce tushen nasara.

 

 

Marubuci: Buhari Abba

Daga: Jahar Kano.

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...