Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Sirikina Ne Ya Cancanta Ya Gaje Ni – Gwamna Okorocha

0 154

Gwamnan jahar Imo, Rochas Okorocha ya bayyana sirikinsa mai suna Uche Nwosu a matsayin wanda ya fi cancanta ya gaje shi a 2019.

Nwosu dai shine mijin ‘yar Okorocha ta fari mai suna Uloma.

Okorocha ya yi wannan magana ne yayin da ya karbi bakuncin shuwagabannin jam’iyyar APC, reshen mazabar Owerri, a jiya Litinin, 12 ga watan nan.

A cewar Okorocha “Uche Nwosu mutum ne haziki. Na yi bincike akan shi ciki da waje, ban samu wata matsala tattare da shi ba. Ba shi da girman kai, a don haka mulki ba zai rude shi ba. Duk da mukamin da ya ke rike da shi, ba ya fada da kowa, ba ya zaluntar kowa kuma ba ya nuna wariya”.

KARANTA WANNAN: A karo na farko, Rochas Okorocha ya soki lamirin shugaba Buhari

Nwosu dai a yanzu haka shi ke rike da mukamin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Imo.

Sai dai kuma duk da wannan magana ta Okorocha, Nwosu bai bayyana aniyar shi na tsayawa takarar shugabancin jahar ba.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...