Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Tirr!: Nijeriya Ta Shiga Cikin Jerin Ƙasashe 10 Da Suka Fi Yawan Karuwai A Duniya

0 518

Karuwanci, da a da ko a kasashen da addini ya ke da karancin mutunci, sana’a ce ko kuma tafarki da al’umma ke tir da shi. Duk wata karuwa, a kowace al’umma, a wancan lokaci ba ta ƙima da mutunci a cikin al’ummarta

 

Sana’ar karunwanci da ma ita kanta mai yin sana’ar ababen ƙyama ne. Ita kanta karuwa ba ta iya bayyana sana’arta a fili a da, kuma ita kanta tana jin zafi ka kirata da sunan karuwa

 

Sai dai kuma a yau abubuwa sun sauya. Kunya da mutunci sun yi ƙaranci. Rashin mutunci, rashin kamala da fitsara sune cinyewa da burgewa ta yadda karuwai suka samu ‘yan cin su yi yawo da trana tsaka suna tallata hajarsu. Karuwai a yau suna zama a cikin mutane, a cikin gar kuma mutanen gari sun san sana’arsu. Kai wasu ƙasashen ma nemawa karuwai samun cikakkiyar ‘yan ta yadda za su ci karensu babbu babbaka ba tare da tsangwama ba wai duk da sunan ‘yanci

 

Wannan yanayi shi ya kawo mu halin da mu ke ciki a yau na samun ƙasarmu Nijeriya a cikin jerin ƙasashe 10 da suka fi yawan kilakai a duniya

 

Ga ƙasashen ta tsarin yawan karuwai:

  1. Venezuala:- ƙasar na da adadin karuwai 119 a kowace mace10,000
  2. Koriya Ta Kudu:- ƙasar na da adadin karuwai 110 a kowace mace 10,000
  3. Peru:- ƙasar na da adadi karuwai 102 a kowace mace 10,000
  4. Philippines:- ƙasar na da adadin karuwai 85 a kowace mace 10,000
  5. Nijeriya:- ƙasar na da adadin karuwai 63 a kowace mace 10,000
  6. China:- ƙasar na da adadin karuwai 60 a kowace mace 10,000
  7. Barazil:- ƙasar na da adadin karuwai 53 a kowace mace 10,000
  8. Maleshiya:- ƙasar na da adadin karuwai 52 a kowace mace 10,000
  9. Jamus:- ƙasar na da adadin karuwai 49 a kowace mace 10,000
  10. Taylan:- ƙasar na da adadin karuwai 45 a kowace mace 10,000
Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...