Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Tunatarwa: Sunnoni Guda 5 A Lokacin Kiran Sallah

Tunatarwa: Sunnoni Guda 5 A Lokacin Kiran Sallah

0 323

Mai gaskiya ‘Yar mai gaskiya Nana A’isha (R.A) Matar Annabi SAW tana cewa:
“Yana cikin babbar asara mutum ya ji Ladan yana kiran Sallah, amma bai bi amsawa mai kiran Sallar ba”.

Ibn Qaiyim Allah ya yi masa Rahama yana cewa: “Akwai sunnoni guda biyar tabbatattu lokacin kiran Sallah”.

1-SUNNA TA FARKO-(1).
“Amsawa mai kiran Sallah wato ka rika fadar abinda mai kiran Sallah yake fada lokacin kiran Sallah”.

DALILI AKAN HAKA
Fadar Annabi SAW:

Idan Ladan ya.ce
” ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ “.
ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, sai dayan ku yace: ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ “.
ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, sannan idan Ladan yace:
” ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ”
“ASH’HADU AN LAA ILAHA ILLALLAH”,sai yace
ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ”
“ASH’HADU AN LAA ILAHA ILLALLAH”, idan ladan yace:
” ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ”
“ASH’HADU ANNA MUHAMMADAR RASULILLAH” Sai ya ce:
” ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ”
“ASH’HADU ANNA MUHAMMADAR RASULILLAH” idan Ladan yace:
” ﺣﻲ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺼﻼﺓ ”
“HAYYA ALAS SALLAH” sai yace:
” ﻻﺣﻮﻝ ﻭﻻ ﻗﻮﺓ ﺇﻻ ﺑﺎﻟﻠﻪ ”
“LAA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAH”,idan yace:
” ﺣﻲ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻔﻼﺡ ”
“HAYYA ALAL FALAH” sai yace
ﻻﺣﻮﻝ ﻭﻻ ﻗﻮﺓ ﺇﻻ ﺑﺎﻟﻠﻪ ”
“LAA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAH” idan yace:
” ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ “.
ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR,sai dayanku yace: ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ “.
ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR,idan yace:
ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ”
“LAA ILAHA ILLALLAH”,sai yace
ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ”
“LAA ILAHA ILLALLAH” wanda yace LAA ILAHA ILLALLAH” azuciyarsa ya shiga aljanna).
@ ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ .
2-SUNNA TA BIYU-(2)
“Yin Salati ga Annbi SAW bayan kare kiran Sallah”.

DALILI AKAN HAKAN.
Manzon Allah SAW yana cewa:
“idan dayan ku yaji kiran Sallah to ya fadi irin abinda mai kiran Sallah yake fada, sannan ya yi Salati a gareni, domin wanda ya yi min salati guda daya Allah zai yi masa guda goma”.
@ ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ .
3-SUNNATA TA UKKU-(3)
“Rokawa Annabi SAW WASILA a wajan Allah ta hanyar karanta addu’ar da Annabi SAW ya koyar dan roka masa WASILA”

DALILI AKAN HAKA
Annabi SAW yana cewa:
“idan dayan ku ya ji kiran Sallah to ya fadi irin abinda mai kiran Sallah yake fada, sannan ya yi Salati a gareni, domin wanda ya yi min salati guda daya Allah zai yi masa guda goma, Sannan ya roka min WASILA domin ita wani matsayi ne a cikin aljanna, ba ta dacewa da kowa sai ga wani bawa daga cikin bayin Allah kuma ina sa ran nine mai wannan matsayi. Dukkan wanda ya roka min wannan matsayin to ceto na ya tabbata a gare shi).
@ ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ .
ADDU’AR ROKAWA ANNABI S.A.W :-
( ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺭﺏ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﺪﻋﻮﺓ ﺍﻟﺘﺎﻣﺔ ، ﻭﺍﻟﺼﻼﺓ ﺍﻟﻘﺎﺋﻤﺔ . ﺁﺕ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﺍﻟﻮﺳﻴﻠﺔ ، ﻭﺍﻟﻔﻀﻴﻠﺔ ، ﻭﺍﺑﻌﺜﻪ ﻣﻘﺎﻣﺎ ﻣﺤﻤﻮﺩﺍ ﺍﻟﺬﻱ ﻭﻋﺪﺗﻪ )
Wanda ya karanta bayan kiran Sallah citon Annabi SAW ya yabbata a gare shi ranar alkiyama).
Muslim.

4-SUNNA TA HUDU-(4)
“Fadar:
” ﺭﺿﻴﺖ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﺭﺑﺎ ﻭﺑﺎﻹﺳﻼﻡ ﺩﻳﻨﺎ ﻭﺑﻤﺤﻤﺪ ﺻﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺭﺳﻮﻻ “.
“RADHEETU BILLAHI RABBAN WABIL ISLAMU DINAN WABI MUHAMMAD S.A.W RASULAN”
DALILI AKAN HAKA
Manzon Allah SAW ya ce: “Wanda ya fada a lokacin da ya gama jin mai kiran Sallah:-
( ﻭﺃﻧﺎ ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ ، ﻭﺃﻥ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﻋﺒﺪﻩ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ . ﺭﺿﻴﺖ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﺭﺑﺎ ، ﻭﺑﺎﻹﺳﻼﻡ ﺩﻳﻨﺎ ، ﻭﺑﻤﺤﻤﺪ ﺻﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺭﺳﻮﻻ ).
Wanda ya fadin wannann Allah ya gafarta masa zunubansa).
@ ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ .
5-SUNNA TA BIYAR-(5)
“Mutum ya rokawa kansa abinda ya so”

DALILI AKAN HAKA
Daga Abdillahi Dan Amru R.A yace:”Ya Manzon Allah Lallai Ladanai suna samun fifikon lada akan mu, Sai Annabi SAW ya ce:
“Ku rika fadar abinda yake fada lokacin kiran Sallah, idan an gama kiran Sallah sai ku roki Allah za’a amsa maku).
@ ﺳﻨﻦ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ .
Annabi SAW yana cewa:
“Adduar da aka yi tsakanin kiran Sallah da ikama ba a mayar da ita, wato karbabbiya ce”).
@ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ
‘Yan uwa mu yi kokari wajen koyi da wannan Sunnoni da kiran ‘yan uwa akan su yi aiki da ita dan mu kasance cikin masu koyi da bin Sunnar Annabi SAW na gaskiya.
@ ﺍﻟﻮﺍﺑﻞ ﺍﻟﺼﻴﺐ ﻣﻦ ﺍﻟﻜﻠﻢ ﺍﻟﻄﻴﺐ … ﺹ 188

KARANTA: Duba Zikirai Guda Bakwai Mafi Tsada A Rayuwar Musulmi

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...