Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Wace ce Wawiyar Mace?- Ustaz Abdurrashid Adam

0 816

Ga amsoshin da Ustaz Abdurrashid Adam ya bayar da aka tambaye shi wace ce WAWIYAR MACE? Amsar tasa ta bayyana wace ce mace wawiya.

Ya ce:

 • Wawiyar mace ita ce wacce in mijinta ya bata kudin cefane bata karba hunnunta bibbiyu tare da godiya
 • Wawiyar mace ita ce bata yabon mijinta a dukkan gwanintar da ya yi mata
 • Wawiyar mace ita ce wacce bata yin ado da kwalliya don mijinta ya gani
 • Wawiyar mace ita ce wacce ba ta yi wa dangin mijinta kyauta, musamman mahaifiyar mijin ko mahaifinsa ko kannensa ko yayyensa
 • Wawiyar mace ita ce ta ke musu da mijinta
 • Wawiyar mace ita ce ta ke daga muryrta sama da muryar mijinta
 • Wawiyar mace ita ce wacce sai a lokacin da mijinta ya shirya tsaf don ya tara da ita, za ta ce masa tana bukatar ta shiga ban daki don ta yi fitsari ko kashi
 • Wawiyar mace ita ce in mijinta na jima’i da ita sai ta kwanta ta mimmike kamar wata gawa ba tare da yin wani salo da zai ja hankalin mijin ba
 • Wawiyar mace ita ce mace kazama
 • Wawiyar mace ita ce wacce ba ta kula da dan kamfan mijinta da gajerun wandunansa da duk wasa kananan kayan da ya ke sanyawa a ciki
 • Wawiyar mace ita ce macen da ta ke iya yi wa mijinta sata
 • Wawiyar mace ita ce macen da za ta iya cin amanar mijinta

Ubangiji ya karemu daga auren wawiyar mace!

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...