Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Wane ne Wawan Namiji???- Ustaz Abdurrashid Adam

0 952

Bayan da Ustaz Abdurrashid ya bayyana wace ce wawiyar mace, matashin Malamin ya sake dawowa don ya yi fashin baƙi kan wane ne WAWAN NAMIJI?

 

Ga yadda Malam ya fasalta WAWAN NAMIJI:

 • Wawan Namiji, shi ne wanda ba ya yabon matarsa idan ta yi kwalliya
 • Wawan Namiji, shi ne mutumin da ya ke baƙin cikin bawa matarsa kuɗ in cefane bayan yana da halin bayarwa
 • Wawan Namiji, shi ne wanda ba ya iya tashin matarsa su yi nafila a tsakar dare
 • wawan Namiji, shi ne wanda ba ya wasa da dariya da matarsa
 • Wawan Namiji, shi ne wanda ba ya shigowa gida da sallama
 • Wawan Namiji, shi ne wanda bai damu da sayawa matarsa kayan kwalliya da gyaran gashi ba alhali yana da hali
 • Wawan Namiji, shi ne wanda ba ya mutunta surukansa
 • Wawan Namiji, shi ne wanda ba ya kyautata mu’amalarsa da ‘yan uwan matarsa
 • Wawan Namiji, shi ne wanda ya ke ɗaukaka amaryarsa sama da uwargidansa
 • Wawan Namiji, shi ne wanda ke raba kan iyalinsa ta hanyar nuna musu bambamci
 • Wawan Namiji, shi ne wanda ke yin riƙon sakainar kashi da haƙƙoƙin matarsa
 • Wawan Namiji, shi ne wanda ba zai iya samar da lokacin da zai raka matarsa asibiti ba in bata da lafiya
 • Wawan Namiji, shi ne wanda ba ya tsoratar da matarsa wuta, baya kwaɗaitar da ita aljanna
 • Wawan Namiji, shi ne wanda bai damu da koyar da iyalinsa ilimin addini ba
 • Wawan Namiji, shi ne wanda baya sanya ido akan yadda iyalinsa ke gudanar ibada ta yau da kullum

BUDE KA KARANTA: WACE CE WAWIYAR MACE?

Allah ya kare ‘ya’yanmu da ƙannenmu da yayyenmu da auren WAWAN NAMIJI, amin

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...