Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Wani Dan Nijeriya Ya Yi Alkawarin Biyan Duk Wanda Ya Yi Rajistar Zabe Wasu Adadin Kudade

0 177

Wani dan Nijeriya ya haifar da cecekuce a shafukan sada zumunta bayan da ya yi alkawarin biyan duk wanda ya yi rajistar zabe tsakanin Juma’ar da ta gabata da Juma’a mai zuwa a jahohi biyar na yankin Kudu maso gabashin kasar nan wasu ‘yan kudade.

Mutumin mai suna Tochukwu Ezeoke ya ce zai biya N1000 ga kowanne mutum daya da ya yi rajistar a matsayin kudin mota da na shan ruwa yayin da ya ke bin layin yin rajistar.

Ya ce abunda ya ke bukata kawai shine shaidar yin rajistar da bayanan asusun bankin mutum, wanda ya ce za a iya aika masa ta sakon Twitter.

Wannan batu dai ya sanya ‘yan Nijeriya da dama sun bayyana ra’ayoyinsu. Yayin da wasu ke ganin hakan bai dace ba, wasu suna ganin hakan ya yi daidai.

Ezeoke ya ce ya yi haka ne kawai saboda ya karawa matasa karfin gwiwar yin rajistar, wanda hakkin su ne a matsayin ‘yan kasa.

KARANTA WANNAN: PDP ta yi korafi akan tsadar tikitin zaben kananan hukumomi a jahar Kano

Ya ce akwai tazara mai yawa tsakanin adadin yan Nijeriya da wadanda suke da rajistar yin zabe, kuma abunda ya nufa da biyan kudin shi ne ya zaburar da mutane su yi abunda ya kamata.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa Nijeriya na daya daga cikin kasashen da ke da mafi karancin adadin masu rajistar zabe.

A shekarar 2001, kaso 50.3 ne ke da rajistar wanda ya sanya Nijeriya a gida na 157 a cikin kasashe 169 a wannan fanni.

Adadin ya ragu zuwa kaso 43.65 a zaben 2015, inda a ciki kaso 32.11 ne kawai suka yi zabe.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...